FIFA Ta Fiytar Da Sunayen ‘Yan Wasa Goma Domin Zama Gwarzon Duniya

‘Yan wasan Faransa da suka lashe gasar cin kofin duniya da suka hada da Kylian Mbappe da Antoine Griezmann da Raphael Barane na cikin jerin ‘yan wasa 10 da za su fafata wajen lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta FIFA.
Kazalika Hukumar kwallon kafar ta Duniya, FIFA, ta sanya sunayen zaratan ‘yan wasa biyu da suka saba lashe wannan kyauta, wato Christiano Ronaldo da Lionel Messi cikin jerin ‘yan wasan.
Har ila yau, akwai Luka Modric na Croatia da Eden Hazard na Belgium da Kebin De Bryne shi ma daga Belgium da aka zaba cikin wadanda za su yi takarar karbe kyautar.
FIFA ba ta mance da zaratan ‘yan wasa irinsu Harry Kane na Ingila da Mohamed Salah na kasar Masar a cikin masu takarar ba.
Sai dai babu sunan dan wasan Brazil da ke taka leda a PSG, wato Neymar cikin jerin ‘yan wasan wanda hakan yakawo cece kuce musamman ashafukan sada zumunta na twitter.
A bangare guda, kocin Faransa Didier Deschamp da Zinedine Zidane na cikin wadanda za su fafata wajen lashe kyautar gwarzon koci a bana.
Deschamp ya lashe kofin duniya, shi kuma Zidane ya jagoranci Real Madrid wajen lashe gasar zakarun Turai sau uku a jere.

Exit mobile version