• English
  • Business News
Friday, August 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fina-finai Masu Dogon Zango A Masana’antar Kannywood: Ci Gaba Ko Akasin Haka?

by Rabilu Sanusi Bena
6 months ago
in Nishadi
0
Fina-finai Masu Dogon Zango A Masana’antar Kannywood: Ci Gaba Ko Akasin Haka?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A wani bincike da kafar yada labaran BBC Hausa ta fitar, ya yi nuni da irin ci gaban da aka samu na zamani a Masana’antar Kannywood.

Kamar dai yadda aka sani ne, yanzu an koma kasuwancin fina-finan Hausa ta manhajar intanet, musamman ma ‘YouTube’ da sauran kafafen sadarwa. Kazalika, wani abu da mutane ke gani kamar sabon abu ne; shi ne yadda a yanzu ake shirya fina-finai masu dogon zango da ake iya shafe tsawon shekara daya zuwa biyu ko ma fiye, ba tare da kawo karshen labarin fim din ba.

  • Ci Gaban Masana’antar Kannywood: Ganin Kitse Ake Wa Rogo – Mai Sana’a
  • Maryam CTV Ta Nemi A Dinga Nuna Al’adun Bahaushe Maimakon Na Wasu Kasashen Waje A Fina-finan Kannywood

Kamar dai yadda aka sani ne, yanzu an koma kasuwancin fina-finan Hausa ta manhajar intanet, musamman ma ‘YouTube’ da sauran kafafen sadarwa. Kazalika, wani abu da mutane ke gani kamar sabon abu ne; shi ne yadda a yanzu ake shirya fina-finai masu dogon zango da ake iya shafe tsawon shekara daya zuwa biyu ko ma fiye, ba tare da kawo karshen labarin fim din ba.

Daga cikin abubuwan da kafar ‘YouTube’ ta kawo Masa’antar Kannywood, akwai dawo da harkokin fina-finai, ta yadda jarumai da dama da aka daina jin duriyarsu a can baya, yanzu suka fara dawowa da karfinsu.

Sai dai, wasu na ganin fina-finan da ake haskawa a ‘YouTube’ din sun fara yawaita, wanda a cewarsu; fina-finan da ke kan ‘Youtube’; sun fi wuyar sha’ani wajen kallo ga masu karamin karfi, duba da cewa an fi kallon irin wadannan fina-finai da ke kan ‘YouTube’, da manyan wayoyin salula.

Labarai Masu Nasaba

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

A watan Janairun wannan shekara ta 2025, an fara fitar da sabbin fina-finan Hausa masu dogon zango sama da 10, wadanda ake nunawa a tasoshin ‘YouTube’ daban-daban, bayan wasu da yawa da aka kwana biyu ana haskawa ta kafar.

Manyan fina-finai, musamman masu dogon zango da kamfanin Saira Mobies ke daukar nauyi, mai suna Labarina; na daga cikin fina-finan da ke kan gaba a ‘YouTube’, harkokin fina-finan Kannywood, sun koma wannan kafar ne; tun bayan da tattalin arzikin masana’antar ya tabarbare sanadiyar mutuwar kasuwar CD, sai ake tunanin komawa ‘YouTube’ din zai inganta kasuwancin masana’antar kamar yadda yake a baya.

An dade ana shirya fina-finan Hausa masu dogon zango, amma fim din Izzar So, na Lawan Ahmad; na cikin wadanda suka fara jan hankalin masu shirya fina-finan masana’antar, inda yanzu kusan duk manyan furodusoshi suka koma haska fina-finansu a kafar.

A baya can, a kan nuna fim babba ne a duk rana, amma yanzu fina-finan sun yi yawan da dole a haska biyu ko sama da haka, wanda hakan yasa wasu ke cewa, suna shan wahala wajen kallon fina-finan, ganin yadda fina-finan masu dogon zango ke kara yawaita, sai wasu ke ganin hakan a matsayin ci gaba, a gefe guda kuma, wasu ke cewa sun yi yawa.

A rahoton na BBC Hausa, za a iya kallon yawaitar fina-finan a matsayin ci gaba, sannan a gefe guda kuma za a iya kallon hakan a matsayin koma baya, ci gaba ne wajen samar da ayyukan yi ga jarumai da sauran ma’aikata da kuma bai wa ‘yan kallo damar samun sabbin fina-finai a koda-yaushe.

Amma yawaitar yin fina-finan, zai iya taba ingancinsu; sakamakon gaggawar fitar da su, Hausawa na cewa, “Idan dambu ya yi yawa, ba ya jin mai.” Sannan kuma, za su iya cunkushewa a kasuwa a rasa samun wanda zai yi babbar nasara, sai dai, masu sharhi na cewa, akwai bukatar a hada karfi da karfe wajen ganin an rika fitar da manyan fina-finai masu ma’ana da za su yi tasiri, su kuma samar da kudaden shiga; maimakon yin fina-finai barkatai da ba su da ma’ana ko inganci.

Wani abu da mutane ke gani shi ne, yawaitar fina-finan zai toshe hanyoyin samun kudi ga masu shirya fina-finan, tunda masu kallo za su raba hankalinsu wajen neman wane fim za su mayar da hankali su kalla, hakan zai sa su kasa tsayawa wuri daya wajen kallon, ma’ana maimakon a yi awa daya ana kallon fim guda, sai a raba wa fina-finai uku mintuna ashirin-ashirin; don a samu a kalli kowane daga ciki, musamman ma mata.

Idan kuma hakan ta faru, akwai yiwuwar ‘YouTube’ ya biya kamfani kudi kalilan, dalili kuwa shi ne; ‘YouTube’ na duba yawan masu kallo da kuma yawan lokacin da suka bata wajen kallon, domin kwatanta abin da ya kamata su biya a kan wani abu da aka dora a kan ‘Youtube’ din.

Maimakon fim daya ya samu ‘yan kallo kamar misali dubu dari biyar, sai ka ga bai fi dubu dari zai iya samu ba, saboda watakila akwai wasu fina-finan da yawa da masu kallon za su so su kalla a dan kankanin lokacin da suka ware, domin kallon fina-finan.

Haka kuma, yawaitar fina-finan manyan furodusoshi na matukar yin tasiri wajen durkushewar kananan furodusoshi masu tasowa, domin kuwa; kananan furodusoshi ba su da kudin da za su dauki nauyin fim din da za a iya shafe shekaru ana haska shi, sannan kuma ba lallai ne ya kasance da mabiya masu yawa a shafinsa na ‘YouTube’ ko wata kafar yanar gizo da za su kalla ba, ballan tana har ya samu wani abin kirki.

Har ila yau, akwai kuma bukatar a samu tsayayyen tsari wanda zai rika kididdige fina-finan da za a haska, domin ‘yan kallo su san su, su kuma san wanne za su bibiya tare kuma da shirya kallon nasu.

Dangane da inganci kuwa, masana sun tabbatar da cewa; akwai bambanci tsakanin fina-finan Hausa masu dogon zango da na kasashen waje, masana’antar fina-finan Hausa; ba su dade da fara mayar da hankali wajen fina-finai masu dogon zango ba, inda tuni sauran kasashen kuma, misali kamar Amurka da Indiya, suka riga suka yi nisa.

Don haka, salon rubuta fina-finai da ingancin aiwatar da su; ko shakka babu, ya sha bamban nesa ba kusa ba, har ma yadda ‘yan kallo ke daukarsu; ba zai taba zama daya ba.

Sai dai kuma, sun ce akwai bukatar masu shirya fina-finan na Hausa, su kara dagewa wajen inganta ayyukansu, domin kuwa akwai wadanda harkar fim, ba sana’arsu ba ce, sai kawai su ce za su shige ta gaba-gadi, kuma sai ka ga babban jarumin Kannywood, ya shiga sun yi fim mara inganci tare da shi, wanda ko alama hakan bai dace ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KannywoodZango
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kwamfutar Quantum Ta Kasar Sin Ta Samu Masu Ziyara Sama Da Miliyan 20 Daga Sassan Duniya

Next Post

Kasar Sin Ta Kammala Gina Jirgin Ruwan FPSO Na Farko Na Duniya Mai Karfin Rikewa Da Adana Iskar Carbon

Related

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa
Nishadi

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

5 days ago
Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa
Nishadi

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

3 weeks ago
Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau
Nishadi

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

4 weeks ago
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
Nishadi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

4 weeks ago
Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda
Nishadi

Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda

1 month ago
Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)
Nishadi

Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)

1 month ago
Next Post
Kasar Sin Ta Kammala Gina Jirgin Ruwan FPSO Na Farko Na Duniya Mai Karfin Rikewa Da Adana Iskar Carbon

Kasar Sin Ta Kammala Gina Jirgin Ruwan FPSO Na Farko Na Duniya Mai Karfin Rikewa Da Adana Iskar Carbon

LABARAI MASU NASABA

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu

July 31, 2025
Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka

Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka

July 31, 2025
NIN-SIM: Masu Hulda Da Kamfanonin Sadarwa Sun Koka Kan Katse Layinsu Daga Tsarin Kira

Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba Da Rajistar Sabon SIM – NIMC

July 31, 2025
Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

July 31, 2025
Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

July 31, 2025
Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

July 31, 2025
Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

July 31, 2025
Gwamnatin Borno Ta Nada Kwamitin Aiwatar Da Mafi Karancin Albashi

Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu

July 31, 2025
Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

July 31, 2025
Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

July 31, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.