Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya kaddamar da asibitin sojoji na kasar dake garin Bishoftu na jihar Oromia, a jiya Asabar.
Ana ganin sabon asibitin wanda kasar Sin ta samarwa tallafin kayayyakin lafiya tare da horar da ma’aikatansa, a matsayin mafi inganci cikin asibitocin kasar.
- Yadda Nake Iya Aika Sako Ta Hanyar Rubuta Labari Yana Saka Ni Nishadi – Mardiyya
- Huawei Zai Tallafa Wa Ci Gaban Fasahar Nijeriya Ta Hanyar Zuba Dala Miliyan 15 Duk Shekara
Yayin kaddamarwar, Abiy Ahmed ya bayyana asibitin a matsayin na musammam, bisa la’akari da kayayyakin kiwon lafiya masu inganci dake amfani da fasahohin zamani da yake da su.
Ya ce asibitin zai samar da hidimomin kiwon lafiya masu inganci da a baya ake ganin ba za a iya samu a cikin kasar ba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)