Connect with us

KASASHEN WAJE

Firaministan Rasha Ya Kamu Da Korona

Published

on

A shekaran jiya ne agogon wurin, Firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ya sanar yayin zantawa da shugaba Bladimir Putin na kasar ta Rasha ta kafar bidiyo cewa, sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa, ya kamu da cutar Korona.

Wannan ya sa, ya ba da shawarar cewa, mataimakinsa na farko Andrey Belousob, ya rike mukamin Firaministan kasar na wucin gadi, a lokacin da ya kebe kansa a gida.

Tun farko, wata sanarwa da shafin yaki da yaduwar Korona na kasar ta Rashan ya fitar da misalin karfe 10 da mintuna 35 na safiyar ranar 30 ga watan Afrilu agogon wurin.

A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kara samun mutane 7,099 da aka tabbatar sun kamu da Korona a Rasha, baya ga sama da 100,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, adadin da yanzu ya kai 106,498.

Akwai kuma sabbin mutane 1,333 da aka sallama bayan sun warke daga cutar, adadin mutane 11,619 da suka warke daga cutar sai kuma mutane 1,073 da suka mutu.

Cutar ta kuma harbi mutane 53,739 a birnin Moscow, wurin da cutar ta fi Kamari a kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: