Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jaddada bukatar kafa managarcin tsarin kasuwar jari mai tsaro, da bin cikakkun ka’idoji, mai gudanar da komai a bayyane, budaddiya, mai tafiya da sauye-sauye, da juriya.
Li, ya yi kira da a kara azamar samarwa kasuwar jari ikon samar da riba, da gaggauta gina kasa mai karfin hada-hadar kudade, wanda zai taimaka wajen zamanantar da kasar Sin.
Firaministan na Sin ya yi tsokacin ne yayin taron nazari na majalisar gudanarwar kasar Sin, wanda ya mayar da hankali ga batun zurfafa gyare-gyare ga kasuwar jari, domin wanzar da ci gaba mai nagarta da daidaito. (Saminu Alhassan)