Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga mahalarta taron kasa da kasa game da bunkasa ci gaba na kasar Sin, da su karfafa kwarin gwiwa, da daidaita burikan da ake da su, ta yadda za a kai ga shawo kan hadurra da kalubale dake addabar tattalin arzikin duniya.
Li wanda ya yi wannan kira cikin jawabin sa ga wakilan kasashen waje, mahalarta dandalin na CDF na shekarar 2023 da ya gudana a birnin Beijing, ya ce Sin za ta kiyaye dokokin bunkasa cinikayya, da tattalin arzikin kasa da kasa, da kara bude kofofin ta ga duniya, da kyautata yanayin kasuwa daidai da tsarin kasuwannin duniya, bisa doka da kiyaye ka’idojin kasa da kasa.
Taron na bana dai ya hallara jagororin siyasa na kasashe masu ruwa da tsaki, da shugabannin manyan kamfanonin duniya 500, da kwararru da manyan masana daga cibiyoyin ilimi na kasa da kasa, da kuma wakilan manyan hukumomin kasa da kasa.
Wakilan kasashen waje mahalarta taron, sun bayyana gamsu game da yadda kasar Sin ta cimma muhimman nasarori a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, sun bayyana cewa, kamfanonin kasa da kasa sun ci gajiya daga sauye sauyen da Sin ke aiwatarwa, da kara bude kofa da saurin ci gaban kasar.
Har ila yau, wakilan sun yi amannar cewa, Sin za ta ci gaba da kara bude kofofin ta, tare da ba da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)