Daga Bello Hamza
A wannan lokaci mafi yawan jama’a sun zama ‘yan kwangila a harkar aikin gwamnati ko na kamfanoni masu zaman kansu, lokacin cin bilis a aikin gwamnati ya wuce. Ma’ana lokacin da aiki ke jiranka da zaran ka gama karatu, aiki na dindindin har zuwa lokacin ritaya na shekara 65, lokacin da zaka koma gefe ka ci gaba da karɓan fansho har iyaka rayuwarka, wannan tsari ya canza matuƙa tun daga shekarar1980.
Saboda haka ya kamata waɗanda ke da aikin gwamnati ko na kamfanoni masu zaman kansu dama waɗanda ke neman aiki a fannoni daban daban su fanhinci cewa kiɗa ya canza domin haka dole rawar su ma ta canza.
A wannan lokacin da ma’ikatu ke fuskantar ƙalubale daban-daban, kamar buƙatar rage ma’aikata, saboda ɓullowar na’urori masu ƙwaƙwalwa da suke maye gurbin aiyukan da mutane ke yi da kuma yadda hukumomi kanfanoni ke ƙoƙarin ganin sun samu cikkakiyar riba da kuma gogoriyo na neman wuce tsara tsakaninsu, ya zama dole ya zamana kai ne ke neman aiki ba aiki ke nemanka ba. Saboda haka takardar tsarin bayanin rayuwarka da matsayin karatunka (Curriculum Ɓitae) tare da takardar neman aikinka ya zama yana tsare tsaf kuma a gaban ma’aikatar da kake neman su ɗauke ka aiki, kada ka jira aiki ya neme ka, saboda tuni aiki ya daina neman ma’aikata, yanzu neman aiki ake yi wurjanjan!
A ƙasar Birtaniya, a shekar ta 2013 akwai mutane miliyan da ke ƙarƙashin wani tsari da ake kira “Zero Hours” wanna tsari ne da wata hukuma mai harkar ɗaukar wa hukumomi da kamfanoni maaikata kan ɗauki mutum, bayan an tantance shi an ba shi takardar shaida an kuma karɓi bayanan asusun ajiyarsa ta banki amma ba wai kai tsaye ya zama ma’aikacinsu ba ne, za dai su neme shi ne a duk lokacin da suke buƙatar aikinsa, a wannan tsarin, babu ruwan hukumar ma’aikatan da ɗawainiyar lafiya ko wani harkar ƙaro ilimi akan irin karatun da ya yi. A wannan tsarin in mutum na son a riƙa buƙatarsa a koda yaushe to dole ya zama mai neman ƙware wa a kan harkar karatunsa da sana’arsa, manya kanfafoni da yawa a Birtaniya irinsu Capita and Group 4 Security ba su da ma’aikata na dindin sai dai su ɗiba daga irin tsarin da muka yi magana a sama, hukumar ilimi ta Birtaniya ma yanzu da irin waɗannan ma’aikata take amfani wajen cike gurbin ma’aikatanta da suka tafin hutun haihuwa “maternity” ko kuma rashin lafiya, wannan tsari na da ma’aikata masu ƙwarewa a fannoni daban-daban, tun daga likitoci har zuwa masu shara.
A wannan tsarin da muke magana a kai dangantakar da ke tsakanin masu aiki da ma’aikaci ya danganta ne da abin da kowanne zai amfana, a ɗan lokacin da za su yi hurɗa babu ɗaukar ɗawainiyar ma’aikaci ta kowanne fanni abin da mai ɗaukan aiki ke nema wajen ma’aikaci shi ne kawai “aiki”, a kan haka kuma shi me neman aiki dole ya bunƙasa kansa a fannonin da ya shahara domin gamsar da masu ɗaukar aiki, ya kuma samar da dangantaka mai gwaɓi tsakaninsa da masu ɗaukar aiki ya kan kuma kasance zama a shirye domin kama aiki a koina kuma a koda yaushe.
Abin tsokaci a nan shi ne dole matasanmu su shirya fuskantar irin wannan tsarin da ya samu gindin zama a ƙasar Birtaniya dama wasu ƙasashe a nan Afirika, saboda a bayyane ya ke cewa gwamnati da kanfanonin da muke da su ba zasu iya samar da aiyukan yi ga ɗinbin matasanmu dake shigowa kasuwar neman aiki a kowanne shekara (Labour Market) ba.
Tuni dai wani masannin halayyar danAdam da ake kira Theodore Rooseɓelt ya yi nuni da cewa “dole mai neman aiki ya fuskanci karɓar aikin wucin gadi ya kuma ƙoƙarin ƙarfafa harkar sanaarsa da na tafiyar da rayuwarsa saboda ‘yan kwadagon daga cikinmu ne za su samu aiki tabbataciya na gwamnati ko na wani kamfani”
Shafi na musamman domin ma’aikata da aikinsu