Sauyin shugabannin rundunonin tsaro da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar a wannan mako zai haifar da murabus da ritayar fiye da janarori 50 daga rundunar Soji, bisa ga tsarin da ke tilasta manyan hafsoshi da suka fi sabon shugaban shekaru su ajiye aiki.
Bayan naɗin Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Shugaban Rundunar Soji (Chief of Defence Staff), tare da sabbin shugabannin rundunonin ƙasa, da sama da manyan hafsoshi 50 da suka yi aiki tare da tsohon CDS, Janar Christopher Musa, za su tafi ritayar dole. Wannan ya haɗa da brigediyoyi, da janarori, da kwamandoji daga Sojojin ƙasa da na sama, da kuma na ruwa.
- Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
- Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa wannan tsarin “Ritayar Doke” yana da tarihi a cikin rundunar, amma sauyin da aka yi a wannan karon na iya shafar ƙwararrun hafsoshi da suka daɗe suna aiki. Wani tsohon kwamandan Soji, Janar Aliyu Gusau (mai ritaya), ya ce irin waɗannan sauye-sauye suna da amfani wajen sabunta rundunar, amma ya kamata gwamnati ta samar da tsarin tallafi ga waɗanda ake tura wa ritaya da wuri.
Wani binciken da jaridar Leadership Hausa ta gudanar ya nuna cewa mafi yawan waɗanda ke shirin ritaya sun fito ne daga rundunar sojin ƙasa, inda ake ganin sabbin naɗe-naɗen za su buƙaci sabon tsarin horo da maye gurbin manyan da zasu bar aiki.
Wasu ƙungiyoyin tsofaffin sojoji sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sabunta tsarin fansho da walwalar masu ritaya, musamman ganin cewa akasarin waɗannan hafsoshi sun yi hidima tsawon shekaru 30 zuwa 35. Kungiyar Veterans for National Security ta ce “akwai buƙatar samar da tsarin taimakon gaggawa domin tabbatar da cewa waɗannan tsofaffin jarumai ba su fuskanci matsin tattalin arziƙi ba bayan ritaya ba shiri”
Sauyin shugabannin tsaro dai ya nuna matakin da Tinubu ke ɗauka wajen sake fasalin tsaro, amma kuma ya buɗe sabon babi na tattaunawa kan yadda ake kula da tsofaffin hafsoshin da suka ba ƙasa hidima tsawon shekaru.














