Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), na horar da manoma kiwon kifi tsawon watanni 12, yayin da a yanzu ta ke wata na shida da bayar da horon, wanda za a ci gaba da aiwatar da shi bayan dawowa daga hutun shekara.
An shirya shirin ne don inganta kiwon kifi da kuma bai wa manoma sabbin dabaru da za su taimaka musu su dogara da kansu.
- An Nuna Wasu Fina-finai Biyu Na Kasar Sin A Najeriya
- Ƴansanda Sun Zafafa Farautar Mambobin Ƙungiyar Asiri Ta ‘Sai Malam’ A Sakkwato
Shugaban ƙungiyar masu kiwon kifi ta jihar, Malam Nura Uba Ramadan, ya yaba da wannan shiri, inda ya bayyana cewa horon ya taimaka sosai.
Ya ce da dama daga cikin manoma ba su ilimin sanin adadin abincin da kifi ke buƙata ko girman ramin da ya dace.
“Amma daga wannan horo, mutane sun san komai da kuma hanyoyin da kiwon zai inganta,” in ji shi.
Wakiliyar FAO, Aisha Ibrahim, ta ce an gudanar da shirin a jihohi daban-daban kamar Kano, Kwara, Gombe, Delta da Osun, don ya amfanar da masu kiwon kifi daga kowane yanki.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka horar, Ibrahim Sulaiman, ya nuna wa mahalarta abubuwan da ya koya da yadda yake amfani da su wajen kiwon kifi.
Kamfanin Vetsark, ya samar da ƙwararrun malamai da suka jagoranci horon har zuwa ƙarshen shirin, kamar yadda jami’in cibiyar, Ajayi Mayowa, ya bayyana.
Mutane kusan 100 ne suka amfana, inda aka raba su gida-gida guda biyar don sauƙaƙa koyarwa da kuma bin diddigin kowane rukuni.
Shirin ya samu tallafi daga ƙungiyoyi kamar FISH4ACP, Tarayyar Turai (EU) da BMZ domin tabbatar da nasararsa.














