Daga Idris Aliyu Daudawa,
Hukumar kula da hana hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa shi Lasisin tuka mota wanda aka ba direbobi ba wai sai wadanda suka mallaki motoci ba, amm duk ‘yan Nijeriya wadanda sukla kai shekarun da za su iya tuki suma suan iya mallaka
Mista Adebisi Olajide, kwamandan FRSC da ke kula da lasisin tuki a Ore Unit Command, ya yi wannan bayani a ranar Talata a Ore, jihar Ondo.
Olajide, wanda ya zanta da manema labarai, ya bukaci ‘yan Nijeriya da suka kai shekarun tuki, da su tabbatar sun wuce makarantun tuki don lasisin tuki.
“Mutane da yawa suna tunanin cewa lasisin tuka mota ya na nufin wadanda suka mallaki motocin ne kawai ya dace su samu.
“Wannan ba haka bane, amma duk wanda ya kai matakin daya dace ace ya fara kuma a shirye yake, ya wuce kuma ya ci dukkan gwaje- gwajen tuki zai iya kokari ya samu lasisin tuka mota.
“Lasisin tuka mota ya zama katin shaida ga mai rike da shi saboda duk bayanansa suna kan sa.
“Hakan kuma zai iya ba su damar tuka abubuwan hawa a duk lokacin da suka samu dama, ba tare da jami’an tsaro sun kame su ba cewar Olajide.”
Ya, duk da haka, ya bukaci duk wanda ke da niyyar bayarwa ko sabunta lasisin tuki da ya bi ta Hukumar FRSC ya daina yin fushi da masu talla wanda zai iya sanya su cikin matsaloli masu tsanani.