Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYINMU

Fyaɗe A Sansanin ‘Yan Gudun Hijra?

by Tayo Adelaja
October 28, 2017
in RA'AYINMU
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Rahotannin baya-bayan nan dake ci gaba yawo a tsakanin al’umma game da yadda masu aikata fyaɗe ke cin karensu babu babbaka abin takaici ne ƙwarai. Koda yake ba wannan ne ma babban abin tashin hankalin ba, face irin yadda waɗannan miyagun mutanen ke yaɗa Cutar Sida (HIV) a sasanonin ‘yan gudun hijiran dake sassa daban-daban, musamman yankin Arewa maso Gabas.

Wannan shafi ya sha yin kira ga gwamnati sau fiye da shurin masaki game da irin halin taskun da ‘yan gudun hijirar ke ciki da kuma irin buƙatun da suke biɗa daga gwamnatoci na gaggawa domin kauce wa abin da ka iya faruwa musamman ga mata da kuma ƙananan yara waɗanda su ne jibge a sansanonin.

Tabbas wannan lamari ne mai tayar da hankali ainun, musamman yadda alƙaluma suka bayyana cewa a yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira kimanin milyan uku dake gararamba a sansanonin ‘yan gudun hijirar a yankin Arewa maso Gabas kaɗai! Sannan kimanin kashi biyu bisa ukun ‘yan gudun hijirar na shaƙe ne a Jihar Borno, jihar ta fi jin jiki daga hare-haren Ƙungiyar Boko Haram.

Koda yake ya zuwa wannan lokacin, rundunar sojin Nijeriya tare da haɗin gwiwar sojin Ƙasashen Kamaru, Chadi, Beni da kuma Nijar sun kakkaɓe kusan dukkan ikon kame wurare da ‘ya’yan ƙungiyar ta yi, tare kuma da samun nasarar ƙwato mutane masu yawan gaske da ƙungiyar ke garkuwa da su, da suka haɗa maza da mata da kuma ƙananan yara.

Duk da cewa sashen bada agajin gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN-CERF) ya tallafa wa ‘yan gudun hijirar da kuɗi har dala milyan 13, don samar da abinci, tufafi, makwanci da kuma kiwon lafiya, amma duk da haka rahotanni na bayyana cewa kusan babu wani canji sahihi na ku zo mu gani da tallafin ya taɓuka, musamman bisa irin zargin da ake yi na karkatar da kayakin daga musu alhakin kulawa da su.

Irin hotunan dake nuna yanayin ‘yan gudun hijirar da ake ta yaɗawa a kafafan yaɗa labarai sun zo wa Shugaba Muhammadu Buhari da ma sauran shugabannin ƙasashen duniya da mamaki, musamman idan aka yi la’akari da irin maƙudan kuɗaɗen da aka yi narkarwa don kyautata wa ‘yan gudun hijirar, irin su Aliko Dangte, TY Danjuma da sauran attajirai da dama, amma ko kaɗan lamarin ya gaza samun nasarar da ake buƙata.

Rahotannin da wasu likitoci na (DWB) suka bayyana, ya nuna cewa kimanin ‘yan gudun hijira fiye da dubu 24 ne ke cikin matsanancin hali da suke buƙatar matakin gaggawa ta fuskar lafiya kawai, yayin da  aƙalla yara kimanin 30 ke mutuwa a kullu yomin cikin sansanonin ‘yan gudun hijirar.

Haka zalika dukkan hoɓɓasar da Hukumar Agajin Gaggawa ta Nijeriya (NEMA) take yi don sauƙaƙa lamurra a sansanonin musamman ma ɓangaran abinci da magunguna, lamarin ya ci rura sakamakon zargin rashawa da ake ga wasu jami’an nata, sannan da kuma rashin isassun kayan bada agajin wadda hukumar ta sha kokawa.

A wani ɓangaren kuma, Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya yi ta kokawa game yadda wasu ƙungiyoyi ke yamaɗiɗi da tataccun hotunan ‘yan gudun hijira dake bayyana su cikin mawuyacin hali su riƙa aikewa da su a shafukan Intanet don janyo hankulan attajirai a sassan duniya don samun tallafi, amma babu gaskiya ko kaɗan a lamarin nasu. “Ba nufi ne in soki wata ƙungiya da take da zimmar taimakawa ba, amma dai lallai abu ne da na sani game da waɗansu ƙungiyoyi na jabu, waɗanda suke amfanin da waɗansu hotunan da suka tace marasa kyan gani, suke sanya wa a kafafan Intanet don neman taimako alhalin ba taimakawar suke ba, damfara ce kawai.” In ji shi.

Koma dai mene ne haƙiƙa ‘yan gudun hijira na cikin mawuyacin halin da suke buƙatar taimakon gaggawa, yayin da kuma a kullum ake samun miyagu a tsakanin sansanonin suna aiwatar cuwa-cuwa, fasadi, fyaɗe da musgunawa iri-iri. Bugu da ƙari ma shine yadda wasu rahotannin ke kausasa zargi ga akasarin ma’aikatan agajin da gwamnatoci ta naɗa don kula da ‘yan gudun hijirar, inda zargin ya nuna cewa da gangan jami’an ke jinkirta maida ‘yan gudun hijirar ga garuruwansu don kawai su ci gaba da samun garaɓasar kayayyakin da suke karkatarwa da sunan ‘yan gudun hijirar.

Don haka lallai Gwamnatin Tarayya da na jihohi musamman na yankin Arewa maso Gabas lokaci ya yi na sake fasalin shirin tallafawa ‘yan gudun hijirar bakiɗaya, ta yadda za a kawo ƙarshen halin matsatsi da ‘yan gudun hijirar ke ciki tare kuma da gaggauta mayar da su matsugunansu na asali don samun kawanciyar hankali sannan ‘ya’yansu su koma makaranta kamar yadda aka saba.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Yunwa Ta Yi Sanadiyyar Rasuwar Yara 120 A Kaduna

Next Post

Yadda Aka Tsinci Jaririya Sabuwar Haihuwa A Kebbi

RelatedPosts

Kannywood

Alhakin Shiga Tsakanin ’Yan Kannywood Da Afaka Ya Rataya A Wuyan Ganduje

by Muhammad
2 weeks ago
0

Masana sha’anin shari'a suna cewa, da a yi kuskuren hukunta...

Dambarwar Najeriya Cikin Shekaru 60: Murna Ya Kamata Mu Yi Ko Kuka?

Yayin Da Nijeriya Ta Cika Shekaru 60 Da ‘Yancin Kai…

by Muhammad
5 months ago
0

A jiya ne Nijeriya ta yi bikin cika shekaru 60...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Cibiyar Jinkan Tsofaffi – Minista Sadiya

Kafa Hukumar Kula Da Nakassasun Nijeriya Da Dawo Da Martabarsu

by Muhammad
6 months ago
0

A ranar Litinin, 24 ga Agusta na 2020 ne, Shugaban...

Next Post

Yadda Aka Tsinci Jaririya Sabuwar Haihuwa A Kebbi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version