Cikin wasu kwanuka da suka gabata, na yi katarin ganawa da kwamishinan kidayar jama’a da gidaje na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim tsanyawa, wanda shi ne zai jagoranci yadda za a tafiyar da sabgar kidaya a wannan jiha tamu ta Kano mai albarka. Hakika, kyawawan shirye-shiryen da a yanzu haka ke bisa teburinsa, na son wayar da kan jama’ar Kano, tare da ankarar da su tarin alfanun da ke tattare da wannan kidaya da ake shirin aiwatarwa cikin wannan Shekara ta 2023, abin a yaba ne matuka da gaske. Bugu da kari, duk wani mutum da ke kishin wannan jiha tamu ta Kano, wajibinsa ne ya dafawa wannan zakwakurin kwamishina, don ganin an aiwatar da harkar kidayar cikin nasara, tare da begen jihar ta Kano, na, ta ci gaba da rike kambunta, na jihar da ta fi kowace jiha dandazon tarin jama’a jibge cikinta, kamar yadda Kidayar Jama’a da Gidaje ta karshe da aka gudanar cikin wannan Kasa ta hakaitar cikin Shekarar 2006.
Kidayar Jama’a Da Gidaje A Nijeriya
Idan za a yi maganar Kidayar Jama’a da Gidaje (National Census) a wannan Kasa, dole ne a yi wa sabgar kallo iri uku ne. Domin kuwa, an fara gudanar da kidayar ne tun gabanin hade Kasar wuriguda a Shekarar 1914, tare da rada mata suna Nijeriya. Sannan, kashi na biyu na kidayar, an aiwatar da shi ne bayan Turawan mulkin mallaka na Birtaniya sun hade Kasar wuriguda. Kashin karshe na kidayar kuwa, an gudanar da shi ne bayan Kasar ta sami ‘yancin-kai daga masu jajayen kunnuwa.
Rukunin farko na aiwatar da kidayar cikin wannan Kasa kafin a kira ta da Nijeriya, an yi ne a cikin garin Lagos da sauran garuruwan da ke kewaye da ita, a Shekarun 1886, 1871, 1881, 1891 da Shekarar 1901. Rukuni na biyu na kidayar, bayan hade daukacin Kasar wuriguda, an yi ne cikin Shekarar 1962/63. Bayan samun ‘yancin kai kuwa, an gudanar da kidayar cikin wannan Kasa ne a Shekarun 1962/63, 1973, 1991 da kuma Shekarar 2006.
Babu shakka, batun kidayar jama’a da gidaje a tarihin wannan Kasa, cike yake da kalubale iri daban-daban daga mabanbantan bangarorin Kasar da mabanbantan kabilunta. Sakamakon haka, sai kabilanci, bangarenci, yarfen siyasa, banbancin addini da sauran banbance-banbance suka mamaye kafatanin sabgar kidayar, ta yadda aka gaza samun wata kidayar da ta karbu dari bisa dari daga daukacin jama’ar Kasar, ba tare da zafafan korafe-korafe ba. Sai dai, akan sami saukin muhawara da kace-nace tattare da wata kidayar sama da wata. Misali, kidayar jama’a ta Shekarar 2006, ta sami karbuwa sama da kidayar jama’a da aka gudanar a Shekarar 1962/63. Kamar yadda tarihi ya hakaitar cewa, mummunan bijirewa sakamakon kidayar jama’a ta Shekarar 1962/63, na daga dalilan da suka taimaka wajen haifar da Juyin Mulkin Soja na farko da aka yi cikin wannan Kasa, na Watan Janairun Shekarar 1966 (January, 1966).
Girmamar Lamarin Kidaya A Duniya, 1950s
Saboda muhimmanci da kuma alfanun da ke tattare da batun kidayar, sai aka wayigari Majalisar Dinkin Duniya ta samar da wata hukuma (United Nations Statistics Dibision, UNSD) sukutun a Shekarun 1950s, don ciccida tare da sanya-idanu game da sha’anin Kidayar Jama’a da Gidaje a daukacin Duniya bakidaya. Wannan hukuma, ta karfafi tare da daga likkafar sha’anin kidayar a Duniya ne, ta hanyar nuna muhimmanci gami da tarin alfanun da al’uma kan girba a fannonin rayuwa iri daban-daban, sakamakon samun cikakken bayanin adadinsu a cikin Kasashensu. Majalisar ta Dinkin Duniya, ta nemi akalla duk bayan Shekaru goma (10) ne ya dace kowace Kasa a Duniya ta sake sabunta kidayar jama’arta da kuma gidaje bakidaya.
Kidaya Ta Karshe A Nijeriya, 2006
Duk da shawarar da Majalisar Dinkin Duniya, UN, ta gabatar cewa, a rika aiwatar da irin wannan kidayar jama’a da gidaje, “census” a duk bayan Shekaru goma (10) a kowace Kasa, sai ya zamana cewa, tsakanin kidaya ukun karshe, 1973, da ta biyun karshe, 1991, a Nijeriya, an sami tazarar Shekaru sha-takwas (18) ne cifcif a tsakaninsu, maimakon tazarar Shekaru 10. Bugu da kari, daga kidayar karshe da aka gabatar cikin wannan Kasa a Shekarar 2006 zuwa yau (2023), an sami tazarar Shekaru goma sha-bakwai (17) ne cifcif. Wannan tazara ta Shekaru 17, za ta tabbata ne idan an gudanar da kidayar jama’a a Kasar cikin wannan Shekara ta 2023 da muke ciki, kamar yadda gwamnati ke cewa za ta yi. Amma idan ya zamana gwamnatin ba ta gudanar da kidayar ba, to fa lissafin tazarar zai kere ko zarta Shekaru 17n ne, zuwa yadda lamura suka kaya.
Na’am, duk da cewa kidayar jama’a ta Shekarar 2006 ta dara sauran takwarorinta karbuwa a wajen jama’ar wannan Kasa, hakan bai hana samun wasu ‘yan korafe-korafe daga jama’ar arewaci da kuma kudancin Kasar ba. Bayan kammala kidayar ta 2006, ya tabbata cewa, jihar Kano ce ta kere daukacin jihohin Kasar yawan jama’a, inda aka sami zunzurutun mutane har kimanin miliyan tara da dubu dari hudu (9. 4m) a cikinta. Jiha ta biyu a yawan jama’a ita ce jihar Lagos, wadda ta rabauta da tarin mutane har miliyan tara (9. 0m) a cikinta. Ke nan, tsakanin jiha ta farko da ta biyu (Kano da Lagos) a batun kidayar, an sami fifikon mutane dari hudu (400) ne daidai wa daida.
Wancan “kambu na fifiko” ne a tun farkon wannan rubutu ake jan-hankalin al’umar jihar ta Kano, na, su ci gaba da rike shi kamkam, duba da irin tarin alhairan da ke tattare da shi ta kowace fuska a rayuwa, muddin gwamnatin taraiya za ta yi la’akari da cikakkun manufofi da abubuwan ake son cimmawa, ta hanyar gudanar da kidayar a tsakanin al’umar Kasa. Domin kuwa, a ilmance kamar yadda za a dan gabatar a nan gaba cikin wannan rubutu, duk wani bangare da zai kyautata rayuwar jama’ar kowace Kasa ce a Duniya, ba ya samuwa cifcif bisa kiyasi na daidai, face ta hanyar gudanar da ingantacciyar kidaya ta adalci da aka aiwatar a cikin Kasa. Bugu da kari, duk jihar da ta kere saura wajen samun dandazon mutane a cikinta, lazim ne ta fi kowacce rabauta da ababen more rayuwa da za su inganta rayuwar mutanenta ta yau da kullum.
A dai waccan kidaya da aka ta Shekarar 2006, gabadaya adadin jama’ar wannan Kasa, ya kama miliyan dari da arba’in ne, da dubu dari hudu da talatin da daya, da dari bakwai da casa’in (140, 431, 790 m) cifcif. A dai cikin sakamakon kidayar, adadin maza a Nijeriyar lokacin, sun kama miliyan saba’in da daya ne, da dubu dari uku da arba’in da biyar, da dari hudu da tamanin da takwas (71, 345, 488 m) cifcif. Adadin rukunin mata a Kasar kuwa, ya kama miliyan sittin da tara ne, da dubu tamanin da shida, da dari uku da biyu (69, 086, 302 m) daidai wa daida.
Rayuwar Al’umma Na Kyautatuwa Ne Ta Hanyar Kidayar Jama’a Da Gidaje
Babban hadafi da kuma manufar gudanar da kidayar al’uma da gidaje a duk inda ake aiwatar da ita a fadin Duniya, bai wuce don inganta mabanbantan bangarorin rayuwar mutane ba. Bangaren ilmi, lafiya, samar da wutar lantarki, samar da gidaje, kasuwa da kasuwanci, harkar tsaro, harkar noma, samar da ababen more rayuwa, samar da kayan agaji, kirkirar kyawawan manufofi na gwamnati da makamantansu, duka ba sa samuwa cikin nasara kuma a wadace, ba tare da gudanar da kidayar jama’a da gidaje ba. Idan kuwa haka ne, ita kanta rayuwar ma, ba za ta tafi cikin nasara yadda ake da bukata, ba tare da aiwatar da kidayar akai-akai ba. Domin kuwa, ta hanyar kidaya ne kawai, za a iya gane adadin mutane kaza ne kunshe cikin Nijeriyar, da sauran jihohi 36 hada da birnin taraiya na Abuja. Jihohi irinsu Bayelsa da Jigawa, ba su wuce adadin wasu kananan hukumomi biyu zuwa uku (2—3) cikin guda arba’in da hudu (44) da suke a jihar Kano ba. Ta yaya ne rabon arzikin Kasa zai daidaita, ba tare da sanin hakikanin kunzumin jama’ar da kowace jiha ta ke da shi ba?
Harkar Ilimi A Nijeriya
Babu shakka mai karatu ya sani cewa, adadin malaman makarantun firamare, sakandire da kuma na jami’a da jihar Kano da Lagos ke da bukatar su samu, ya kere adadin yawan adadin malaman da ake da bukata a jihohin Bayelsa da Jigawa da ma Katsina. Gwamnatocin wadannan jihohin da aka lasafto, ta hanyar sanin adadin mutanensu kadai ne, zai sa su fahimci adadin wadanda za su koyar a irin wadannan makarantu nasu.
Da jihar Kano za ta yi la’akari da lissafin da jihar Jigawa ko Bayelsa za ta yi, wajen samar da malaman makaranta a jihohinsu, babu shakka da Ilimi ya sami mummunan kazgaro a Kanon, duba da irin tarin tazara ta al’uma da ake da su a tsakanin mabanbantan jihohin uku. Ba ya ga malamai, hatta adadin gine-ginen makarantu da ake da bukata da kuma yunkurin samar musu da kayan aiki, zai matukar banbanta ne da juna tattare da jihohin. Mu dubi shirin ciyarwa na gwamnatin taraiya ga daliban makarantun firamare, tallafin ciyarwar da gwamnatin ta taraiya ya dace ta bai wa mabanbantan jihohin Kasar, ba tare da gudanar da sabuwar kidaya a Kasar ba, yaya bayar da tallafin zai zamto bisa sikelin adalci?. Yanzu tallafin ciyar da yaran firamare da jihar Yobe ko Maiduguri ke son amsa daga gwamnatin taraiya, zai yi daidai da tallafin da jihar Lagos ke son amsa?. Ko ba a yi wannan tambaya ba, mai karatu zai fahimci wawakeken gibi na fifikon al’uma da ke a tsakanin wadannan jihohi uku da aka ambata. A fili yake cewa, ba tare da gudanar da sahihiyar kidaya a Kasa ba, babu wani bangare na rayuwar al’uma da zai tafi sumul kalau bisa diga-digansa.
Mu dauki misalin adadin yara da matasa da ba sa zuwa makaranta, ko aka kore su daga makaranta, ba tare da sanin hakikanin adadinsu ba, ta yaya ne gwamnati za ta fito da wata sabuwar manufa da za ta magance irin wadannan matsaloli?. Shin, gwamnati za ta kara gina wasu ajujuwa ne ta mayar da su makarantun, ko kuwa gwamnati na da tunanin budewa matasan cikinsu wararen koyon sana’o’i ne, ko ma menene shirin gwamnati a kansu, muddin ba ta da cikakken lissafinsu a hannu, to fa akwai yiwuwar yin aikin baban giwa, ko lissafin dokin rano, matacce da rayaiye!!!.
Hatta wani kasafin kudi da gwamnatin taraiya ko ta jiha za ta yi a sabgar Ilimi, sanin hakikanin adadin daliban makarantu, da kuma wadanda ake sa-ran dauka a makarantun, na da gayar muhimmanci a tattare da gwamnati. Shin, mai karatu bai san da cewa, yawan jama’a na da matukar tasiri ba, hatta wajen fifikon lissafin kasafin kudi a mafi yawan lokuta ba. Mu yi duba mana zuwa ga tazarar kasafin kudi a harkar Ilimi da ke a tsakanin jihar Kano da jihar Yobe ko Maiduguri. Babu shakka, tarin yawan makarantu da ‘yan makaranta, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun mamakon fifikon kasafin kudi a bangaren ilmi da jihar Kano ke da shi sama da jihohin Yobe da Maiduguri.
Da a ce gwamnatin taraiya ko wata ta jiha a Nijeriyar yau, za ta dawo da dadaddiyar manufar bai wa yara ‘yan firamare litafan makaranta da kayan makaranta kyauta tamkar irin yadda ya gudana a can baya cikin wasu Shekaru a wannan Kasa, lissafin abinda jihar Kwara za ta kashe dole ya banbanta da abinda jihar Lagos za ta kashe. Daga manyan dalilan da za su tilasa jihar Lagos kashe kudi sama da jihar Kwara, akwai batun fifikon yawan jama’a da ake a tsakanin jihohin biyu. Bugu da kari, a sani cewa, yawan jama’a ko karancinsu da wata jiha ke da shi sama da dayar, tilas dole na da bukatar gudanar da kidaya don samo bakin zaren yadda za a yi a tallafi wannan al’uma a zamanance.
Tamkar irin yadda aka dan yi fashin-baki game da alfanun kidayar jama’a da gidaje a fannin ilimi, haka abin yake a sauran bangarorin rayuwar al’uma da aka lasafta a baya.