Gabon Za Ta Fara Fitowa A Finafinan Nollywood

Fitacciyar jarumar nan ta finafinan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a finafinan Kudancin Nijeriya wanda aka fi sani da Nollywood.

A wata hira da aka yi da ita a kafar sadarwa BBC Hausa, Gabon ta ce ta fara gwada sa’arta a finafinan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin finafinai a bangarori daban-daban.

A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun finafinan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a finafinan Nollywood.

“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos Real Fake Life’.

“Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a finafinan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim”.

Hadiza Gabon ta kara da cewa, “Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al’adata ba”.

Jarumar ta ce babu wani, “bambanci tsakanin yadda ake yin finafinan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe ba. Don haka na ji dadin soma fitowa a fina-finan Nollywood.”

 

 

Exit mobile version