A bisa umarnin Shugaban ‘Yansandan Kasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ga dukkan sassan ‘Yansandan Nijeriya domin su ƙaddamar da shirin aiki na rage laifuka, kwamishinan ‘Yansandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, bayan fara aiki a ranar 17 ga Maris, 2025, ya inganta dabarun leƙen asiri da aikin Ƴansanda, tare da tsaurara matakan tsaro domin magance sabbin barazanar da aka gano.
Sakamakon wannan mataki, an samu nasara mai babba wanda ta haifar da kama mutane 10 da ake zarginsu da aikata laifukan satar mutane da satar kudi, kuma an samu nasarar ƙwato kuɗi, da makamai, da kayan aiki daga hannun waɗanda ake zargi.
- Ƙasar Sin Ta Yi Alƙawarin Ƙarfafa Hulɗar Da Ke Tsakaninta Da Kano
- Sarkakkiyar Zargin Da Gwamnatin Abba Ke Wa Ganduje
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘Yansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sa hannu, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin a lokuta daban-daban tun daga ranar 18 ga Maris, 2025.
A cikin binciken da aka gudanar, an samu bindiga da harsashi daga hannun waɗanda ake zargi, ciki har da AK-47 da Beretta, da kuma motoci da aka sace. Haka kuma, an kwato kuɗi Naira miliyon 4.8 daga hannun waɗanda ake zargi da hannu a sha’anin satar mutane da sauran laifuka.
Kwamishinan ‘Yansandan ya yaba wa jami’an da suka gudanar da wannan aiki, inda ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Kano. Dukkanin waɗanda ake zargi suna cikin bincike a sashen binciken laifuka na CID, kuma za gurfanar da su gaban shari’a bayan kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp