Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya bukaci hukuma mai kula da albarkatun ɗanyen man fetur ta ƙasa NNPC, da cewa ta fara ayyukan binciken ɗanyen man fetur a jihar Yobe a ɓangarorin da ke da alaƙa da tafkin cadi. Gwamnan ya ce musamman, saboda yanayin yadda yankunan jihar suka tara-kama da yankunan da aka gano albarkatun ɗanyen man a ƙasashen Nijar da Chadi.
Alhaji Ibrahim Gaidam yayi wannan furucin ne a sa’ilin da ya kai wata ziyara ta musamman a ofishin shugaban haɗakar wannan hukma ta NNPC; Dukta Maikanti Kachallah Baru a’Abuja.
Gwanan ya fara da miƙa buƙatar gwamnatin jihar Yobe da cewa” zan fara da bayyana buƙatar da muke da ita ga hukumar NNPC dangane da binciko albarkatun man fetur ɓangarorin tafkin Chadi waɗanda jihar Yobe tayi tarayya dasu a maƙwabtaka a yankunan Nijar da Chadi. Waɗannan iyakokin ƙasashe da aka gano albarkatun man suna da alaƙoƙi da yanayi na bai ɗaya da namu fake yankin arewa maso-gabas, musamman jihar Borno idan an kwatamta ta da Yobe.”
“Har wala yau, zan doki ƙirji tare da farincikin bayyana muku cewa, a halin da ake ciki yanzu cewa an samu kwanciyar hankali a jihar Yobe, yanayin da kuma zai baku zarafin ci gaba da ayyukan ku na binciko albarkatun man, ba tare da wata barazanar tsaro ba. Domin share fage, gwamnatin mu ta aiwatar da muhimman ayyuka a ɓangarori da dama waɗanda zasu sauƙaƙa muku wasu matsaloli da suka ƙunshi gina hanyoyin mota a kowanne lungu da saƙon da muke kyautata zaton zai shafi ayyukan ku a jihar Yobe.” Ya tabbatar.
Haka zalika kuma, Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam, ya jajanta wa gamayyar hukumar NNPC dangane da hatsarin harin da aka kai wa ma’aikatan hukumar, a kan hanyar su ta zuwa aikun haƙar man fetur; kwanan baya, a jihar Borno tare da yabawa shugaban hukumar bisa ƙoƙarin sake ɗora hukumar albarkatun man fetur bisa ingantattar alƙibla, tun bayan kasancewar sa shugabanta. Tare tabbacin samun goyon bayan gwamnatin jihar Yobe wajen cimma muradun binciko man fetur a jihar.
Da yake maida bayanin sa, shugaban gamayyar hukumar albarkatun man fetur ɗin, Dukta Maikanti Baru, ya fara da bayyana cewa a binciken da suka gudanar na share-fage wanda hukumar NNPC ta gudanar ya tsikayo musu cewa a cikin wasu ɓangarorin gabashin jihar Yobe akwai alamomin samun albarkatun man.
“Daga cikin abubuwan da muka yi la’akari dasu, bisa ga bayanan farko da muka tattara kuma masu alaƙa da gwaje-gwajen da muka aiwatar a cikin waɗannan yankuna dake jihar Yobe..mun samu wasu abubuwa da suka ja hankalin mu a cikin wannan binciken namu a jihar Yobe, kuma shirin da muke dashi shi ne muna begen ganin al’amurran tsaro sun lafa, alabashi sai mu ci gaba da aikin namu”. Inji Maikanti.
Yayin da ya ƙarƙare bayanin nasa da tabbatarwa tawagar gwamnatin jihar Yobe kan cewa hukumar NNPC zata yi iya ƙoƙarin ta wajen ci gaba da gudanar da ayyukan binciko albarkatun ɗanyen man fetur da dangogin ta dake shimfiɗe ya yankin ɓangarorin tafkin Chadi wanda Yobe ta kasance ɗaya daga ciki kuma ba da jimawa ba.