Gamayya kungiyar ‘yan kasuwar Muhammad Abubakar Rimi da akafi kira da Kasuwar Sabon Gari karkashin shugabancin Alhaji Aminu Mu’awiyya Dala sun jajanta wa ‘yan uwansu ‘yan kasuwar kantin Kwari da na kan titin Bairut bisa iftila’in ambaliyar ruwa da rugujewar gini daya jawo samun raunuka da asarar dukiya.
Da yake magana a madadin shugaban kungiyar, jami’in hulda da jama’a na kungiyar Salihu Ibrahim Darma ya ce wannan abu ya damesu a matsayinsu na ‘yan kasuwa wannan abu ya faru ne a sanadiyyar gine-gine da aka yi barkatai ba a bisa ka’ida ba, ana toshe hanyoyi magudanan ruwa.
- Kashi 31 Na ‘Yan Nijeriya Ba Su Iya Karatu Da Rubutu Ba ― Gwamnatin Tarayya
- Gwamna Buni Ya Cika Alkawarin Saya Wa Iyalan Sheikh Goni Aisami Gidaje
Ya kara da cewa duk da sun gamsu da matakinda Gwamnan Kano ya dauka na ba da umurnin gaggawa na rushe duk wani gini da ake ganin shi ya jawo ambaliyar ruwar da aka yi a Kantin kwari sai dai suna kira ga Gwamnati ta sanya yan kasuwa a cikin kwamitinda ta kafa da za su yi aikin rushe gineginen domin su suka san duk wasu gine-gine da akayi da sune musabbabin jawo ambaliyar da Gwamnan bai san dasu ba, muddin ba su aka kawar ba, za a cigaba da samun cigaba da ambaliyar.
Darma ya ce ba kasuwar ta Kantin Kwari kadai ba yawanci kasuwanni da suke Jihar Kano akwai irin wadannan matsaloli na yin gini ba bisa ka’ida ba kuma hakan na faruwa ne da sahalewar hukumomi, hakan tasa yan kasuwar sun yita korafe-korafe da kokawa ga Gwamnati a kan lamarin takai har wasu sun je kotu, amma abin takaici ko bayan da kotu ta bada umurnin a dakatar da gine-ginen sai ayi biris da umurnin a cigaba.
Ya yi nuni da cewa ko a kasuwarsu ta Sabon gari akwai ginegine na toshe hanyoyi da kofofin da hukumar Kasuwar tayi kuma sun kai kuka ga hukumomi har majalisar jiha, amma ba wani mataki da aka dauka akai daga bisani suka je kotu amma ba abinda ya sauya.
Ya yi nuni da cewa irin wannan abin Allah ya kiyaye in wani hatsari ta faru kamar na gobara babu ta inda za a iya kai dauki na gaggawa saboda duk an yi gine-gine da suka toshe hanyoyi.
Darma ya ce yakamata hukumomi su rika daukar mataki akan duk wani jami’in hukuma da ya yi abinda ya sabawa doka da ka iya cutar da al’umma. Tare da yin fatan Allah ya mayar da alkhairi ga yan kasuwar.