Dr. Abdullahi Ganduje, Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, ya yi kira ga haɗa hannu tsakanin shugabannin siyasa domin ƙarfafa ɓangaren shari’a, da kare doka da oda, da kuma kare tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Da yake jawabi a zaman tattaunawa na farko na ƙungiyar shawarar Jam’iyyu (IPAC) da aka gudanar a Abuja mai taken “Matsayin Shari’a wajen ɗorewar Dimokuraɗiyya a Nijeriya,” Ganduje ya jaddada muhimmancin rawar da ɓangaren shari’a ke takawa wajen gina dimokuraɗiyyar ƙasa.
- Gwamnan Kano Ya Kwace Filayen Makarantun Da Ganduje Ya Cefarnar
- Za A Sake Maka Ganduje A Kotu Kan Badaƙalar Naira Biliyan 57.4
Ganduje ya amince da ƙalubalen da ɓangaren shari’a ke fuskanta, wanda ya haɗa da rashin wadataccen kuɗi, da jinkirin gudanar da shari’a, da kuma buƙatar ‘yancin ɓangaren shari’a. Ya bayyana cewa duk da waɗannan ƙalubalen, akwai damarmakin yin gyare-gyare da za su ƙara inganta rawar da ɓangaren shari’a ke takawa wajen ɗorewar dimokuraɗiyya. Ya yi kira da a tabbatar da cewa ɓangaren shari’a ya kasance mai cin gashin kansa kuma ba tare da tasiri daga waje ba.
Sanarwar karshe ta zaman tattaunawar ta buƙaci kotunan Nijeriya da su duba sosai kan ƙa’idojin shari’ar zaɓe da ka iya taimakawa wajen yin magudi da kuma ƙaƙaba ‘yan takarar da aka ki su a zabe.
Mahalarta zaman tattaunawar sun buƙaci a yi gyare-gyaren da za su fifita tanade-tanaden kundin tsarin mulki, da zamanantar da amfani da shaidu na lantarki, tare da sanya tsauraran ƙa’idoji kan Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) game da tura sakamakon zabe.
Haka kuma sun shawarci ɓangaren shari’a da ya nisanci tasirin siyasa sosai, tare da yin tsarin ɗaukar alƙalan kotu bisa gaskiya da cancanta domin tabbatar da mutuncin ɓangaren shari’a.