Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa, akalla mutum 632 ne aka gurfanar a gaban kuliya; bisa laifin lalata kayayyakin gwamnati da wawure dukiyoyin jama’a, a yayin zanga-zangar kuncin rayuwa a jihar.
Mai Magana da yawun Gwamnan Jihar, Sanusi Dawakin Tofa ne; ya tabbatar da gurfanar da wadanda ake zargin a wata sanarwa da ya fitar.
- Shugaban Zanzibar Ta Tanzania: Ba Za Iya Raba Ci Gaban Afirka Da Sin Ba
- Firaministan Pakistan: Bunkasuwar Sin Ya Zama Abin Misali Ga Kasar
Ya bayyana cewa, an cafke mutane 632 da aka gurfanar a ga-ban kotu da laifin lalata dukiyar jama’a a sassan birnin.
Dawakin Tofa ya yi gargadin cewa, kudirin gwamnatin Jihar Ka-no na wanzar da zaman lafiya; ba abu ne da za a tattauna ba, inda ya kara da cewa, wadanda aka samu da laifin barnata dukiyoyin al’umma za su fuskanci fushin doka ba tare da wani bata lokaci ba.
Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta yi shirin samar da dimbin shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i daban-daban, domin inganta dogaro da kai da kuma dakile yiwuwar amfani da su wajen tabarbarewar doka da oda.
Kakakin, ya kuma sanar da cewa; za a kafa kwamitin bincike na musamman da zai binciki wadanda ke da hannu wajen kashe-kashe da sace-sacen gine-ginen jama’a a fadin jihar.
“Hukumar za, ta yi kokarin gano musabbabin kashe-kashe da lalata gine-ginen jama’a,” in ji shi.
Ya bayyana cewa, masu zanga-zangar dauke da tutocin Kasar Rasha ba su da wata alaka ko ta kusa ko ta nesa da gwamnati, don haka; ya bukaci hukumomin tsaro da su bankado wadanda ke sanya su da kuma manufarsu.
A cewarsa, masu zanga-zangar na gaskiya a jihar; sun mika kokensu da bukatunsu ga gwamnati, wanda ya ce za a mika su ga shugaba Bola Tinubu.
Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta yi shirin samar da dimbin shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i daban-daban, domin inganta dogaro da kai da kuma dakile yiwuwar amfani da su wajen tabarbarewar doka da oda.