Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya dakatar da shirin kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta a jihar.
An bayyana wannan mataki ne cikin wata sanarwa da Baffa Babba Dan Agundi, jigo a jam’iyyar APC a Kano, ya fitar.
- Wakilin Sin Ya Sake Gargadin Japan Da Ta Janye Kalamanta Na Kuskure
- Tarayyar Turai Ta Ɗauki Nauyin Shirin Zaman Lafiya Na Yuro Miliyan 5.1 A Zamfara
Shirin kafa hukumar mai suna Hisbah Fisabilillahi, ya jawo ce-ce-ku-ce da damuwa a tsakanin jama’a.
Saboda haka, Gwamnatin Jihar Kano ta hana aiwatar da shirin.
Tun da farko, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana kafa hukumar a ranar 8 ga watan Disamba, 2025, bayan da aka fara raba fom ɗin daukar aiki.
Sanarwar ta ce an dakatar da shirin ne bayan taron masu ruwa da tsaki daga dukkanin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
An yanke wannan shawara ne domin bai wa gwamnatin jihar damar magance batun cikin lumana tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.














