Ganduje Ya Karbi Rahoton Kwamitin Kaddamar Da Shirin RUGA

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa; gwamnatin jihar za ta jajirce wajen ganin ta kaddamar da shirin RUGA a jihar domin ganin an killace makiyaya domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a garin Kano a yayin da yake karbar rahoton dangane da shirin RUGA din da kuma kasuwar madara a Kano.

A cewarsa ba ya batun dakile rashin tsaro, shirin na RUGA zai kawo sauyi a bangaren zamantakewa da tattalin arziki da kuma kare mutuncin Fulani, tare da bude sabon babi ga samun haraji ga gwamnati.

Ya kara da cewa su ma Fulani suna da bukatar abubuwan more rayuwa. Sannan suna da bukatar ilimi. Domin a cewarsa ilimi ginshiki ne. Sannan ya ce gwamnatin na tunanin samar da kwatar yanka dabbobi.

Shugaban Kwamitin, Dr Jibrilla Mohammed, ya ce sun kai ziyara a dazuka har biyar kafin su zabi dajinDansoshiya a karamar hukumar Kiru domin ganin an kaddamar da shirin.

Sauran dazukan sun hada da; Panyabo a Doguwa, Duddrum Gaya a Ajingi, Dunawa a Makoda da kuma Bichi. Ya ce bayan tattaunawa ne, Kwamitin ya zabi dajin Dansoshiya dake karamar hukumar Kiru wajen gudanar da aikin.

 

Exit mobile version