Ganganci Ne Soke Koyar Da Tarihi A Jami’o’in Nijeriya – Farfesa Kurawa

Tarihi

Daga Mustapha Ibrahim,

Wannan shi ne angiza mai kantu ruwa kuma babban ganganci ne da sagegeduwa da kantafi da rayuwar mu ta gobe soke koyar da karatun tarihi a jami’o’in mu da sauran makarantun mu na gaba da sakandire da ma sauran wuraren koyarwa a Nijeriya a ce an daina koyar da tarihi a Nijeriya wannan saki reshe ne kama ganye.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban Jami’ar Maitama Sule dake birnin Kano a Tarayyar Nijeriya Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron walimar zuri’ar Salihi Mustapha Dan Makwayon Kano wanda aka shirya a dakin taro dake Sultan Road a ranar Asabar da ta gabata.

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya kara da cewa su a Jami’ar Maitama Sule dake Kano kasancewar sun san muhimmancin tarihi da alfanin sa ya sa yanzu haka Jami’ar ta samu sahalewar hukuma NUC mai kula da jami’o’i ta Nijeriya cewa yanzu haka suna koyar da tarihi digiri na biyu har digirin digirgir wato PhD a wannan jami’ar domin duk wanda bai san tarihin kansa ba, to yaki ya ci shi domin bai san inda ya fito ba bai kuma san inda za shi ba kaga babu maganar ci gaba a gare shi kuma babu cigaba a duk al’umma da kasar da ba su san tarihinsu ba, domin tarihi shi ne madubin al’umma kuma ginshiki ne na al’umma a kowanne zamani, sannan duk mutum ko wata al’umma da ba ta san a karantar da tarihi to tahirin tane babu kyau mu kuwa al’ummar Arewa da sauran wasu al’ummomi a kasar nan tarihin su na da kyau, mun yi murna da yadda gwamnatin tarayya da sauya tunani akan soke tarihi da aka yi kuma yanzu aka yarda aka dawo da shi da kuma koyar da shi a makarantun Nijeriya.

Har ila yau ya kara da cewa makasudin wannan taro nasu shi ne, alaka da tarihi domin sadar da zumunci na zuri’ar Malam Salihi Mustapha, da kuma tabbatar da cewa wannan zuri’ar ta san kanta har zuwa illa masha Allah ta san kanta kuma muna son al’umma ta yi koyi da shi domin bunkasa zumunci a tsakanin al’umma wanda wannan zuri’a ta Salihi Mustapha ta yi a yau wanda kuma shi ya haifi ‘ya’ya tara ne a duniya, biyu ne rak suka rage a duniya ciki har da mahaifiyarsa Hajiya Zainab wanda ahi jika ne ga Salihi Mustapha kuma abun farin ciki ne ga wannan rana da kuma yabawa marubucin wannan littafi Alhaji Muhammad Datti Salihi wanda ya rubuta littafin tarihin zuri’ar Salihi da aka kaddamar a wannan wuri.

Exit mobile version