Abdullahi Muhammad Sheka" />

Gara Da APC Ta Hana Obaseki Takara – Ganduje

Kasa

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyarsu ta APC ta yi daidai wajen hana takwaransa na Jihar Edo, Godwin Obaseki, izinin sake takara a zabe mai zuwa.

Gwamnan Kanon ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a fadar gwamnatin jihar ranar Litinin.

Ganduje ya ce, jam’iyyar ta bi matakan da su ka dace wajen daukar matakin, kuma su yanzu abinda ke gabansu shi ne, samun nasarar zaben da sabon dan takarar da jam’iyyar za ta tsayar.

Gwamnan ya ce, Jihar Kano za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin Jam’iyyar APC ta lashe kujerar gwamnan Jihar Edo, saboda yadda a ka bi matakan da su ka dace daki-daki.

Amma a nashi bangaren, Gwamnan Jihar Ribers, Nyesome Wike, na jam’iyyar PDP, ya cacaki shugabannin Jam’iyyar APC kan matakin da su ka dauka na haramta wa Gwamna Obaseki takara, inda ya ce, zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin gwamnan ya lashe zabe mai zuwa.

Rahotanni sun ce PDP na zawarcin Obaseki, amma gwamnan ya ce, ba zai yanke hukunci kan makomarsa ba har sai ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari nan gaba.

Sai dai kuma a jiya gwamnan na Edo ya bayar da sanarwar ficewarsa daga APC din bayan ya ziyarci Fadar Shugaban Kasar, duk da cewa, rahotanni sun tabbatar da cewa, bai gana da Shugaba Buhari ba.

Exit mobile version