Connect with us

LABARAI

Gara Na Fadi Zabe Da Na Ci A Cikin Rikici –Gwamna Ortom

Published

on

Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya bayyana cewa, kwanda a ce ya fadi a babban zabe mai zuwa da a ce ya ci zaben na Gwamna da ke tafe a watan Fabrairu mai zuwa ta hanyar rikici.
Gwamnan ya bukaci ‘yan siyasa a Jihar da su guji tayar da kowace irin rigima kafin babban zaben na 2019.
Ortom ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, a Cocin St Bincent De Paul Kuasi Parish, da ke Aliade, kusa da babban birnin Jihar Makurdi, a lokacin da ake jana’izar tsohon Mai Shari’a marigayi Emmanuel Ayargwer.
Ortom yace, sam bai dace ba a shekar da jinin wani saboda ana son a ci zabe, domin ai mulki na Allah ne, shi ne kuwa ke bayar da shi ga dukkanin wanda ya so.
Ya ce, mutanan Jihar sun yanke shawara a kan yin aiki da dokar da ta hana yin kiwoa sarari,da kuma samar da wuraren kiwon na musamman ta 2017.
Gwamnan ya karfafa cewa, al’umman Jihar ta Benuwe ba sa yin kiyayya da kowace kabila, amma dai suna kin duk wanda yake son ya lalata masu shuke-shuken su, wanda shi ne makiyayan suke yi.
Ortom ya nemi da a kara tsaurara addu’o’i domin dorewar zaman lafiya kasantuwan yanda babban zaben 2019 ke ta kara karatowa.
Ya yi addu’an Allah Ya jikan wanda ya rasun, Ya kuma baiwa iyalan sa hakurin jimre rashin na shi.
Kanin mamacin, wanda tsohon mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP ne a Jihar, Dakta Tsetim Ayargwer, ya bayyana jin dadin iyalan ga halartar jana’izan da Gwamna Ortom ya yi.
Ya kuma gode wa Shugaban majami’ar ta, St John’s International, da sauran abokanan siyasar sa kan irin goyon bayan da suke baiwa iyalan a daidai lokacin da suka yi irin wannan babban rashin.
Jagoran Cocin ta, St. Bincent De Paul Kuasi Parish Aliade, Rabaran Fr Aledander Iorhuna, ya bukaci kiristoci da su kasance jakadun Yesu Kiristi nagari, ta hanyar yin rayuwarsu ta hanyar da ya koyar masu, domin su sami Aljanna a bayan sun mutu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: