Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya yi watsi da jia-jitar da ake yi cewa, masu garkuwa sun sako daliban Kwalejin kimiyya Kagara guda 27 da malamai 3 da suka kama ranar Laraba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne, a jiya Juma’a lokacin da yake ganawa da ‘yan jarida a fadar gwamnatin jihar da ke Mina, a jiya Juma’a.
Gwamnan ya ce, an kusa kai wa karshe, wajen tattaunawa da masu garkuwar na ganin cewa, an sako wadannan dalibai.
Malamin addinin Musilincin da ke Kaduna, wanda shiga inda masu garkuwan suke domin tattaunawa da su, Sheik Ahmed Gumi, ya bayyana cewa, ba da jimaea ba, za a sako dalibai da malaman da masu garkuwan suka kama a jihar.