Kasar Japan ta lallasa Kasar Jamus da ci 2-1 mai ban mamaki bayan an dawo hutun rabin lokaci na gasar cin kofin duniya a ranar Laraba.
Tun da farko, bugun daga kai sai mai tsaron gida, Ilkay Gündogan na jamus ya zura wa japan kwallo daya 1-0 bayan da mai tsaron gidan Japan Shuichi Gonda ya buge David Raum, wanda hakan ya jawo fanareti a minti na 33 da fara wasan.
Ritsu Doan ya zura kwallo a ragar Jamus inda yanzun wasan ya zama 1-1 acikin minti 75.
Takuma Asano ne ya dauko wata doguwar kwallo a minti na 84, kuma shi kadai yaje ya zura kwallo ta biyu a ragar Jamus.