Yanzu haka gasar wasan motsa jiki ta Asiya ajin masu bukata ta musamman karo na 4 na gudana a birnin Hangzhou, gasar da ta samu halartar ‘yan wasanni kimanin 3,800 daga kasashe ko yankunan Asiya fiye da 45. Mai masaukin bakin gasar wato Sin, ta mai da hankali matuka kan kyautata na’urorin ba da kulawa ga masu bukata ta musamman kafin bude gasar.
An samar da kujeru, da bayan gida, da matakai da hanyoyi na musamman. Ban da wannan kuma, a kauyen gasar, an samar da gadaje na musamman kimanin 1100, da dai sauran na’urori na musamman, matakan da ya bayyana kulawar da da Sin take baiwa ‘yan wasan.
- Asalin Kungiyoyin Mayakan Hamas, Hizbullah Da Manufofinsu
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Da Ake Iya Sarrafawa Daga Nesa
A hakika dai, Sin na mai da hankali matuka wajen tabbatar da hakkin masu bukata ta musamman a cikin gida, gwamnatoci da kungiyoyin masu bukata ta musamman na wurare daban-daban sun rika kyautata tsarin ba da kulawa gare su, ta yadda za a kara tabbatar da mutuncinsu, da daga matsayin zaman rayuwarsu.
Bisa wani rahoton da aka bayar a shekarar 2023, an ce ya zuwa karshen shekarar 2022, yawan masu bukata ta musamman da aka taimakawa wajen samun ayyukan yi, ya kai fiye da miliyan 9, daga cikinsu yawan wadanda suka kama aiki a bangaren fasaha ya karu sosai.
Daga dokar tabbatar da hakkin masu bukata ta musamman, da taimakawa musu wajen samun ayyukan yi, har zuwa inganta kungiyoyin masu bukata ta musamman. Matakan da Sin take dauka ba ma kawai ya taimakawa ‘yan wasa masu bukata ta musamman a gasar ba, har ma sun taimakawa al’ummar duniya wajen fahimtar kokarin da Sin take yi na kula da masu bukata ta musamman, da tabbatar da hakkinsu. (Mai zana da rubuta: MINA)