Gawuna Ya Taya Gwamna Ganduje Murnar Zama Gwarzon Shekara Ta 2021

Gwarzon Shekara

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

 

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya taya Gwamna Dakta Abdullahi Ganduje murna bisa samun lambar karramawa ta gwarzon shekarar 2021 da Kamfanin Jaridar Punch ta ba shi. Kamar yadda Daraktan Yada Labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hassan Musa Fagge ya shaida wa LEADERSHIP Hausa.

 

Mataimakin gwamnan ya ce “Ka cancanci wannan karramawa, musamman idan aka yi la’akari da yadda jagorancinka na shekara shida ya haifar da gagarumin ci gaban Jihar Kano.

 

“Wannan karramawa da daya daga cikin jaridun da ke fita kullum ta bai wa Gwamna Ganduje wata shaida ce da ke tabbatar da irin ci gaban da aka samu a Jihar Kano.

 

“Ina kira ga jama’ar Jihar Kano da su ci gaba da bada hadin kai da goyon baya ga Gwamnatin Ganduje, domin ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofi da tsare-tsare wanda aka sa ran za su samar da sauyi mai dorewa.

 

Exit mobile version