Manajin Darakta na kamfanin sarrafa Yoghurt dake a jihar Kano Alhaji MD Abubakar ya yi nuni da cewa, dakatar da samar da kudaden musayar ba zai karyawa masu sarrafa Madarar a cikin kasar nan kwarin gwaiwa ba.
Alhaji Abubakar ya kara da cewa, gibin dake a da shi tsakanin kudaden musayar na kasar waje da kuma kasuwar cikin gida ba zai isa a hana shigo da madarra cikin kasar nan ba.
Manajin Darakta na kamfanin sarrafa Yoghurt dake a jihar Kano Alhaji Abubakar ya buga misali da kasar Kenya da ke da kashi 60 a cikin dari na kudin shigo da kaya cikin kasar da ta kakabawa masu shigo da madara cikin kasar ta, inda kuma ya yi nuni da cewa, kashi 15 a cikin dari ana yin amfani da su ne wajen bunkasa fannin samar da madara a cikin kasar, musamman domin a kara habaka tannin na samar da madarar mai dimbin ya wa a kasar nan.
Shi a nasa ra’ayin, wani mai samar da madara a jihar Kwara Ayodotun Ismail, ya goyi bayan ra’ayin Manajin Darakta na kamfanin Alhaji Abubakar.
Idan za a iya tunawa dai, a kwanan baya ne dai, aka ruwaito Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa, nan ba da jimawa zai wanzar da tsarin samar da kudaden musaya na kasar waje don dakile shigo da madara cikin kasar nan, inda bankin ya kara da cewa, Nijeriya ta kai matsayin da za ta iya samar da wadatacciyar madarar a cikin kasar nan.
Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan a wata ganawar da ya yi da manema labarai a Abuja.
A cewar Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya Godwin Emefiele, barin ana shigo da madarra cikin kasar nan ya na kara janyo kasar koma baya, inda kuma hakan ke janyo nakasu ga masu sarrafa a cikin Nijeriya.
Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya Godwin Emefiele ya ci gaba da cewa, duk wanda keda ra’ ayin samar da wajen yin kiwon shanu bankin zai tallafa ma sa da bashi da kuma samar masu da kayan aikin saffara madarar.
Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya Godwin Emefiele ya kara da cewa, Nijeriya ta shafe shekaru sama da 60 tana shigo d madara a cikin kasar nan.
A wata sabuwa kuwa, Jimi’in shirin aikin noma da ke a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya ce, an samar da sabuwar fasahar za ta taimaka matuka wajen kula da amfanin na wake a nahiyar,
A cewar Jimi’in shirin dake a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo, manoman na wake, zasu iya yin amfani da samfarin Irin na (PBR) irin yadda su ke bukatar yin amfani da shi ba tare da samun wata tangarda ba.
Jimi’in Francis Nwankwo, haka manufar kuma ita ce don a tabbatar da ana kula da shi yadda ya dace, tun daga farkon lokacin da aka gudanar da yin gwaji a kansa a dakin yin gwaje-gwaje zuwa masu kimiyya daga nan kuma zuwa gun kamfanonin da zasu sayarwa wa da manoman na wake don kuma su yi amfani dashi a kan gonakan su.
Jimi’in shirin dake a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo, sabon Irin na wake, ba koma zai zamo wani nauyi ga manoman na cowpea ba, inda ya kara da cewa, sai dai ma ya kara masu ilimi da kuma taimaka masu kan yadda zasu yi amfani dashi a cikin sauki.
Don a tabbatar da Irin na cowpea ba’a gurbata shi ba Jimi’in shirin dake a yankin Yammacin nahiyar Afrika Francis Nwankwo ya bayyana cewa, hukumar zata yi kmfani da lambar wayar tafi da gidanka ta (MAS) da shirin ya tanada a matsayin dabarun gano Irin da aka gurbata shi.