Kwanan baya, wakilin musamman na MDD ya kai ziyara gidan kurkuku na Guantanamo, inda ya gano cewa, har yanzu ana yi wa mutane da ake tsare da su a wurin azaba. A cikin shekaru da dama da suka gabata, Amurka ta kafa gidajen kurkuku a wurare daban-daban a duniya inda ta fake da batun yaki da ta’addanci. Alkaluma da aka fidda sun nuna cewa, bayan batun “9.11”, wadannan gidajen kurkuku da ta kafa sun shafi kasashe ko yankuna fiye da 54, inda aka tsare mutane fiye da dubu 100, ciki har da musulmai da mata da yara da sauransu, har an yi wa fursunonni azaba.
Ofishi mai kula da harkokin kasa da kasa da al’umma na jami’ar Brown na Amurka ya taba ba da wani rahoto cewa, mutanen da Amurka ta tsare a wadannan gidajen kurkuku a matsayin ‘yan ta’adda, babu shaidu dake bayyana cewa, su ‘yan ta’adda ne, kuma ba a taba kai su kotu ba. Duk da haka, ‘yan sanda sun yi musu azaba, matakin da ya illata hakkinsu.
Amurka tana tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe bisa ikirarin demokuradiyya da kare hakkin bil Adam, abin da ya keta dokar kasa da kasa. Ya kamata Amurka ta rufe wadannan gidajen kurkuku da yin nadama kan laifukan da ta aikata, da ma rokon gafara da biyan diyya da gurfanar da wadanda suka yiwa mutane azaba a gaban kotu. (Mai zana da rubuta: MINA)