Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce, gidauniyar Qatar Charity Foundation na shirin gina gidaje 500,000 ga wasu marasa karfi a karamar hukumar Chikun da ke jihar.
Sani ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da ya kai ziyarar duba yadda aikin samar da gidajen ke gudana a Sanabil a karamar hukumar, inda tuni aka gina gidaje 100 a karkashin shirin.
- Ranar Nakasassu: Gwamna Uba Sani Ya Nanata Kudirin Shigar Da Su Harkokin Jihar Kaduna
- Tudun Biri: Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Kwamitin Sa Ido Kan Rabon Gudunmawa
Sani ya ce ana gina gidaje 100 a matakin farko na aikin yayin da za a sake gina wasu gidaje a matakai na gaba.
Gwamnan ya ce, za a samar da filin noma da kuma wurin kiwon kaji don samarwa da inganta rayuwa ga marasa galihu da ke zaune a gidajen.
Sani ya bayyana jin dadinsa da yadda aikin ke gudana a wurin, inda ya ce, “ ‘yan watannin da suka gabata, mun zo wurin bikin kaddamar da ginin.
“A yau, na yi farin cikin ganin sakamako mai ma’ana – gidaje da dakunan shan magani da shaguna da gonar kiwon kaji.
“Duk wadannan abubuwan da aka samu sun samu ne daga gidauniyar Qatar Charity Foundation, wanda ke bayar da gagarumar gudunmawa mai girma a Nijeriya, hakika muna godiya da wannan tallafi.”
Sani ya bayyana irin gudunmawar da gidauniyar ta bayar daban-daban, a fannin kiwon lafiya da taimakon marayu da bayar da tallafi ga masu kananan sana’o’i.
Ya ce, “Gidauniyar Qatari tana bayar da tallafin jari ga marayu ’yan kasuwa 5,000, a wani yunƙuri na kawar da talauci a jihar.
“Ayyukan da Gidauniyar Charity Foundation ta yi ya wuce aikin gina gidaje masu yawa, tare da gina rijiyoyin burtsatse a kananan hukumomi daban-daban a fadin jihar don inganta samar da ruwa sha da tsaftar muhalli a yankunan karkara.”