Taron kwamitin amintattu na gidauniyar tunawa da tsohon Firimiyan yankin Arewa Sir Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato wanda aka yi ranar Talata ta wannan makon ya gano matsalolin da suka addabi ci gaban ilimin a Arewacin Nijeriya, inda Shugaba, Sakataren kwamitin amintattu, tsofaffin Ministan ilimi,da sauran masu fada aji da bangaren ilimi.Shugaban kwamitin amintattu tsohon gwamnan Jihar Neja Babangida Aliyu shi ne ya bayyana matslolin da suka hana ilimi a sashen Arewa cigaban daya kamata.
Matsolin da aka gano sun hada da yadda wasu yara ke zama a kasa a makarantu, yawan cunkosun yara, makarantu ba kula da gyaransu wasu ma basu dace ace ana karatu su cikinsu ba.Wasi daga cikin Malaman makaranta suna aikin koyarwar ne saboda basu samu aikin da suke bukatar yi ba, bugu da kari kuma ba kowace makaranta bace ake samun Malaman makaranta da suke da a kalla shaidar kammala kwalejin horon Malamai wato NCE inda aka ce kashi 50 na Malaman da suke koyarwa a Arewa basu da shedar samun NCE ba,wanda shi ne ake son duk Malami ya mallaka ilimi ke nan mafi karanci na koyawa.
- Ba A Kafa NBC Don Takura Wa Kafafen Yaɗa Labarai Ba – Minista Idris
- Rikicin Isra’ila Da Falasdinu: CAN Ta Nuna Damuwa Kan Halin Da Masu Ziyara Na Nijeriya Ke Ciki A Isra’ila
Rashin abubuwan da suka dace a same su a kowacce makaranta domin jan hankali wajen karatu.A Arewacin Nijeriya,inda ya ce shekar 60 bayan rasuwar Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa babu wani ci gaban da aka samu a tsohon sashen na Arewa dangane da al’amarin da ya shafi Arewa.
A fara tunanin gano wuraren da ake samun matsaloli da daukar matakan da suka kamata domin dawowa a irin salon daal’amuran da aka yi shekarun da suka gabata
Bukatar a dauki matakai cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba,inda ya kara da cewa “Abubuwan da aka gano ba ana nufin su sa mu yi kasa a gwiwa ba an son mu kara zage damtse ne somin mu farka daga barci.
Ministan yada labarai da Muhammed Idris cewa ya yi yakamata a fara tunanin gano wuraren da ake samun matsaloli da daukar matakan da suka kamata domin dawowa a irin salo na tafiyar da al’amuran da aka yi shekarun da suka gabata .A fara tunanin gano wuraren da ake samun matsaloli da daukar matakan da suka kamata domin dawowa a irin salon da al’amuran da aka yi shekarun da suka gabata
Yayin da Tsohon Ministan Ilimi Sanata Ibrahim Shekarau ya ce “Sa jari a al’amarin horarwa da kara fasahar ci gaban Malamai abu ne da bai kamata ayi wasa da shi ba, domin zai bada hanya ta inganta hanayar”.
Ba da kudaden da suka kamata wajen ilimi da tabbatar da ana ba shi kulawar da ta dace sai kuma zuba jari shi ma wanda ya dace.