Aƙalla mutum 1,700 ne suka rasa rayukansu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta auku a ƙasar Myanmar, yayin da sama da mutum 3,400 suka jikkata a birnin Mandalay, birni na biyu mafi girma a ƙasar.
Lamarin ya jefa dubban iyalai cikin halin tsaka mai wuya, suna neman mafaka, abinci, da magunguna.
- Shekaru 15, Wasanni 535, Yaushe Kane Zai Lashe Kofi A Ƙwallon Ƙafa?
- Ana Share Fagen Gudanar Bikin Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Shigar Da Su Kasar Sin Yadda Ya Kamata
Ƙungiyoyin agaji sun fara aikewa da kayan tallafi don taimaka wa waɗanda iftila’in ya shafa.
Rahotanni sun bayyana cewa girgizar ƙasar ta yi ƙarfi har ta haddasa rushewar wani gini mai tsayi a birnin Bangkok na Thailand, mai nisan kilomita 1,000 daga inda lamarin ya faru, inda mutane da dama suka maƙale.
Ana kallon wannan iftila’i a matsayin mafi muni da ya taɓa faɗa wa Myanmar tun bayan rikicin siyasar da ya ɓarke sakamakon juyin mulkin soji a 2021, wanda ya haddasa matsin rayuwa da rashin kwanciyar hankali.
Hukumomin Myanmar sun buƙaci ƙasashen duniya su hanzarta tura agaji, yayin da jami’an ceto ke ƙoƙarin gano mutanen da suka maƙale a cikin baraguzan gine-gine.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp