Musa Ishak Muhammad" />

Girmamawa Da Mutunta Kowa Su Ne Silar Nasarorina A Kannywood – Furodusa Yunusa Mu’azu.Girmamawa Da Mutunta Kowa Su Ne Silar Nasarorina A Kannywood – Furodusa Yunusa Mu’azu.

Tattaunawar WAKILINMU MUSA ISHAQ MUHAMMAD Tare Da Furodusa Yunusa Mu’azu Na MASANAANTAR KANNYWOOD.
Da Farko Za Mu So Mu Ji Cikakken Sunanka Da Kuma Takaitaccen Tarihinka.
To ni dai sunana Yunusa Mu’azu, an haife ni ne a Jihar Gombe. Na yi karatuna na Firamare da Sakandire duka a Jihar Gombe.To daga nan sai na dawo nan Jihar Kano kuma na shiga cikin harkar fina-finai. To bayan na fara harkar fina-finai sai na kara komawa makaranta na je na yi (Diploma) a (Purchasing and Supply) daga shekarar 2010 zuwa 2012. Sannan na kara yin wata (Diploma) din a Film and Television Production, a Northwest University wadda a ka fi sani da Jami’ar Yusuf Maitama Sule a yanzu.
Ya Ya A Ka Yi Ka Samu Kanka A Cikin Masana’antar Fina-finai?
To ni dai na samu kaina a cikin harkar fim ne ta hanyar danuwana Kuma yayana wanda shi ya dade ya na shirya fina-finai a cikin wannan masana’anta wato Usman Mu’azu. Tun ya na zuwa da aikin gida ya na yi, sai ya fara cewa in taya shi, shi kuma ya na nuna min yadda zan yi. To a haka ina taya shi ayyuka idan ya zo da su, kawai wataran sai ya zo da wasu ayyuka guda biyu, ayyukan sun hade masa kuma duka sai ya yi su tare. Kawai sai ya ce to ai kai ma Yunusa za ka iya, to shi ne sai ya ce min in shirya in je in yi masa aiki daya a Kaduna, shi kuma zai je ya yi dayan a Minna. Shi ne sai ya kirawo abokan aikin ya fada mu su cewa akwai kanina na turo shi zai kama min aikin. To da na je sai na yi (contunity) wato mai kula da ci-gaban shiri. To daga haka na fara yau da gobe kuma na ci-gaba da yi har zuwa yanzu.

A Wanne Lokaci Ne Ka Fara Aiki A wannan Masana’antar?
Eh to na dade ina tare da masana’antar fina-finai, amma da fara aiki a cikin masana’antar na fara ne a shekarar 2009. To tun daga wannan lokacin ga shi Allah ya na taimakawa tun daga mataki na kasa ga shi a na ta kara yo sama.
A Lokacin Da A Ka Gabatar Maka Da Wannan Aiki Na Farko Da Ka Fara Yi A Kaduna, Wane Irin kalubale Ka Fuskanta Duba Da Cewa Shi ne Aikinka Na Farko A Cikin Masana’antar?
To gaskiya ban fuskanci kalubale ba da yawa, saboda a lokacin nasan aikin tunda ina taya shi danuwana tun a baya. Kuma mafi yawan wadanda mu ka yi aikin tare da su a lokacin duk na san su sun san ni, to sun taimaka min sosai wajen ganin samun nasarar aikin. To a haka dai na yi wannan aikin cikin nasara kuma kowa ya yaba wannan aikin nawa. To tun daga wannan aikin ne fa a ka fara ahh daman wane ya iya aiki haka, to shi ne fa sai na ci-gaba da samun aiki daga bangarori daban-daban. A sanadin haka, kusan gaskiya duk wani fitaccen mai bada umarni a wannan masana’anta wato Darakta na yi aiki da shi a wannan lokaci.
Duk Wanda Ya San Yunusa Mu’azu A Masana’antar Fina-finai, Kusan Ya Sanka Ne A Matsayin Mai Shiryawa Da Kuma Bada Umarni A Cikin Masana’antar, Ya Ya A Ka Yi Ka Fara Shirya Fina-finai Da Kuma Bada Umarni?
To Kamar Yadda na fada dazu, farko dai na fara yin aikin (continuity) ne wato mai kula da ci-gaban shiri, amma daga baya na fara shirya fina-finai. Kuma fim na farko da na shirya fim dina ne, sai danuwana shi ma ya bani fim dinsa na shirya duba da yadda ya yaba wannan fim din nawa da na shirya. To daga nan ne na ci-gaba da shirya fina-finai kuma na mutane daban-daban. To amma duk da haka na fi bada karfi a (continuity) saboda shi na fi iyawa kuma shi na fi so ma a raina a lokacin. To daga nan ina ta yi, sai wasu daga cikin daraktocin su ke bani shawarar cewa ai nima zan iya ba da umarni a cikin fim, tun duk kowa nasan yadda ya ke aiki, kuma na je makaranta na kara sanin abun a ilimance. To bayan na gama makaranta na ba da umarni a cikin wani fim guda daya mai suna “Lantana” daga shi kuma na zo na yi fim din “Ka Yi Min Uzuri”, to zuwa yanzu dai fina-finai guda uku ne na fito a matsayin mai bada umarni a cikinsu.
To Wanne Ne Fim dinka Na Farko Da Ka Fara Shiryawa?
To fim dina na farko da na fara shiryawa shi ne fim din “Matar Hamza”. Fim ne da mu ka yi shi a lokacin da su Ali Nuhu, su Fati Ladan, da su Ali Rabi’u Ali Daddy da dai sauransu.

Duba Da Cewa Wannan Fim Na Matar Hamza Shi Ne Fim Na Farko Da Ka Fara Shiryawa A Cikin Wannan Masana’anta, Wane Irin kalubale Ka Fuskanta A Lokacin Da Ka Ke Shirya Wannan Fim din, Ko Tunda Daman Ka Na Da kwarewa A Cikin Harkar Ba Ka Samu Wani kalubale Ba?
Ai ba zai taba yiwuwa ka yi fim ka ce ka yi shi cikin nasara dari bisa dari ba, dole ne za a dan samu ‘yan matsaloli nan-da-chan. Wani lokacin za ka dan samu kalubale daga abokan aikinka, ko wani abu makamancin haka. Amma lokacin duk da fim dina ne na farko, amma da ya ke ina zaune da kowa lafiya ban samu wata matsala da jarumaina ko wasu daga cikin abokan aikina ba. Amma dai an dan samu kalubale kadan, saboda na sha wahala sosai a lokacin aikin fim din, don wani lokacin ko bacci ba na iya yi a lokacin da mu ke aikin fim din.
A Tsahon Shekarun Da Ka Dauka Ka Na Aiki A Wannan Masana’anta Ta Kannywood, Izuwa Yanzu Fina-finan Da Ka Shirya Sun Kai Kamar Guda Nawa?
Eh to gaskiya na shirya fina-finai sun kai kamar guda goma sha biyu haka. Sannan kuma na bada umarni a cikin fina-finai guda uku. Wannan shi ne a takaice.
To A Cikin Wadannan Fina-finan Da Ka Yi A Tsahon Wannan Lokaci, Wanne Fim Ne Ka Fi So A Cikinsu, Wanda Duk Lokacin Da Ka Tuna Da Shi Ka Ke Jin Dadi Kuma Ka Ke Alfaharin Cewa Kai Ne Ka Yi Shi?
To gaskiya ni duk fina-finan da na shirya ina son su duka. Da wadanda nawa ne na shirya da kuma wadanda wasu ne su ka bani na shirya mu su, da kuma na danuwana da na shirya. To duka ina son duk wani fim da na yi, amma gaskiya na fi son fim din “Matar Hamza” saboda shi ne fim dina na farko da na fara shiryawa. Saboda tun ina tsoro-tsoro a lokacin, kuma har na yi shi cikin nasara. Kuma fim din ya samu yabo sosai, kuma an samu kudi da shi. Kuma har yanzu idan ka na kallon fim din, za ka ga kamar yanzu a ka yi shi. Tun daga irin kayan aikin da mu ka yi amfani da su, zuwa irin kwararrun jarumai da mu ka saka a cikin fim din, da ma kuma yadda Darakta din fim din wato Aminu Saira ya dauki fim din. To wannan fim ina alfahari da shi kuma ba na kunya ko fargabar a kunna shi a ko’ina a kalla, saboda ina alfahari da aikinsa.
A Cikin Wadannan Fina-finan Da Ka Yi Dai, Wanne Fim Ne Ka Sha Wahala Sosai A Aikinsa, Wanda Duk Sanda Ka Tuno Shi Ka Ke Tuna Irin Wahalar Da Ka Sha?
To fim din da ya fi bani wahala shi ne wani fim dina mai suna “Jarumta”. Na sha wahala sosai a lokacin aikinsa. Saboda mu na cikin aikin sai jarumin ya yi tafiya zuwa Legas har wajen kwana 2, wanda hakan ya tilasta dakatar da aikin. Kuma shi daman fim kasan idan ka fara shi kamar ka na sakawa kudinka wuta ne. Saboda kullum cikin kashe kudin a ke, to duk ranar da ta wuce ba a yi aikin ba, to ta zama kamar asara kenan, saboda duk abinda ka kawo zaman kudi ya ke a kowacce rana. To amma a lokacin da jarumin ya dawo sai ya kirawo ni mu ka zauna sannan ya tambaye ni duk asarar da na yi a wannan kwanaki biyu, sai ya bani kudin asarar da na yi sannan washe gari kuma mu ka ci-gaba da aiki. A lokacin ya tausaya min ne saboda ina matshi amma na dakko kudina masu yawa zan yi fim, to shiyasa ya ji tausayina kuma ya yi min wannan kokarin.
Za Mu So Ka Fada Mana Wasu Daga Cikin Fina-finan Da Ka Shirya, Yadda Mai Karatu Ya Na Jin Su Zai Gane Wadannan Su Ne Fina-finan Da Furodusa Yunusa Mu’azu Ya Shirya.
Eh gaskiya mafi yawan fina-finan da na yi fitattu ne kusan kowa ya san su. Na shirya fina-finai kamar irin su Matar Hamza, Yaki Da Jahilci, akwai wani fim ma na barkwanci mai suna Head Master, wanda ni da danuwana Usman Mu’azu mu ka shirya shi, sannan akwai wani fim shi ma mai suna Kishin Balbal shi ma ni na shirya shi, sai kuma wani fim mai suna Ka Yi Min Uzuri, wannan shi ma ni na shirya shi kuma ni na bada umarninsa ma.
Ya Za Ka Bayyana Alakarka Da Sauran Abokan Aikinka A Cikin Wannan Masana’anta?
To ni dai gaskiya ina zaune da kowa lafiya, ba ni da matsala da kowa. Ina mutunta kowa da kowa, saboda kusan ina cikin masu kananin shekaru a cikin wannan masana’anta. Saboda haka dai a takaice ni ba ni da matsala da kowa, ina zaune lafiya da kowa a cikin masana’antar nan a matakai daban-daban.
A Karshe Me Ne Ne Sakonka Ga Masoyanku Masu Kallon Fina-finanku?
Sakona agaresu shi ne, mu na godiya agaresu bisa irin yadda su ke bamu hadin kai idan mun yi fim su na kalla, kuma su na bibiyarmu. Mu na jin dadin hakan kwarai da gaske. Allah ya basu ikon ci-gaba da bibiyar mu, idan mun yi kuma su kalla. Saboda daman ba dan kowa a ke yi ba sai dan su din. Allah ya taimake mu da mu da su baki Daya. Sannan ina kara kira agaresu da su ringa kokarin siyan fina-finanmu na ainihi, ba a gurun masu satar fasaha ba, kuma sannan idan mun kawo fina-finanmu sinima su ringa zuwa su na kalla. Mu na godiya Allah ya bar zumunci.
Furodusa Yunusa Mu’azu Mu Na Godiya Kuma Muna Maka Fatan Alkhairi.
Ni ma na gode kwarai da gaske

Exit mobile version