Akalla mutum 41 ne suka mutu yayin da wasu 14 suka jikkata sakamakon barkewar wutar gobara a cikin wata Coci da ke birnin Giza a kusa da Cairo, kamar yadda hukumar lafiya ta kasar Egypt ta sanar.
Binciken ‘yansandan kasar ya ce wutar gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki.
-  NLC Ta Bukaci Buhari Ya Kara Albashin Ma’aikata Da Kashi 50
- Kasar Sin Ta Mika Wasu Takardun Amincewa Da Yarjejeniyoyi Biyu Ga ILO
Majiyoyin tsaro biyu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa wutar ta barke ne a daidai lokacin da masu Ibada sama da 5,000 ke gudanar da ibadarsu a cikin majami’ar.
An tura injunan kashe gobara har guda 15 a yayin da kuma wadanda suka jikkata aka kwashe su cikin motar daukar marasa lafiya zuwa asibitocin da ke kusa da wajen.
Shugaban kasar Abdel Fattah el-Sisi ya jajanta wa Kiristocin kasar bisa faruwar wannan lamarin.
Daga baya hukumar kashe gobara ta ce an shawo kan gobarar.