Akalla mutane biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu tare da lalata gidaje fiye da 1000 bayan da wata gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri a jihar Borno a ranar Laraba.
Gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 6:00 na safe, ta shafe sama da awa daya kafin jami’an hukumar kashe gobara ta jihar su shawo kanta.
- Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta Kan ‘Yan Ta’adda, Sun Halaka 160 A Borno Da Yobe
- ‘Yansanda Na Bincike Kan Musabbabin Mutuwar Kwamishinan ‘Yan Gudun Hijira Na Jihar Borno
Darakta-Janar na Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Barkindo Muhammad, wanda ya tabbatarwa manema labarai afkuwar lamarin, ya ce, rundunar hadin guiwa ta farar hula, da hukumomin tsaro, da wasu nagartattun ‘yan kasa ne suka taimaka wajen kashe gobarar.
Barkindo ya ce, hukumar ta fara tantance irin barnar da gobarar ta yi don fara shirin bayar da agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.
“Mun fara samar da buhunan shinkafa 500, barguna da sauran kayayyaki domin rage musu radadin wahalhalu,” in ji shi.