Gobara ta kone shaguna sama da 50 tare da kayan miliyoyin Naira a kasuwar bayan Tasha da ke Damaturu, a Jihar Yobe.
Shaidu sun ce wutar ta yadu, wanda ta janyo asara mai yawa kafin jami’an kashe gobara na Damaturu da al’umma su yi nasarar kashe ta.
- Sabon Albashi: NLC Ta Fara Yajin Aiki A Jihohi 15 Na Nijeriya
- An Fara Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro A Nijeriya
Duk da cewar babu asarar rayuka, ‘yan kasuwa sun shiga tashin hankali saboda asarar da suka yi.
Mustapha Gujba, daya daga cikin wadanda abin ya shafa, ya yi addu’ar Allah Ya musanya musu da mafi alheri.
Har yanzu gwamnatin jihar ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba, kuma ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Al’umma sun yi kira da a tallafa wa wadanda abin ya shafa.