Gobara Ta Lakume Ofishin INEC A Enugu

Ofishin INEC

Daga Mahdi M. Muhammad,

Wata gobara ta barke a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke Obollo Afor a karamar hukumar Udenu da ke jihar Enugu.

Lamarin gobarar wanda ta faru a daren ranar Alhamis ta lalata wani bangare na ginin hukumar tare da cinye kayayyakin ofis din da dama da kuma muhimman takardu.

Ba a iya tantance musabbabin tashin gobarar ba, duk amma wasu majiyoyi da ba a tabbatar da su ba sun danganta barkewar da karfin wutar lantarki.

A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda ta jihar Enugu ta tabbatar da barkewar gobarar wacce ta faru a ofishin INEC da ke Obollo Afor, inda ta ce ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar PPRO, ASP Daniel Ndukwe ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka baiwa manema labarai ranar Juma’a a Enugu.

Ya ce, “biyo bayan kiran gaggawa da aka yi a hedikwatar ‘yan sanda na Udenu da ke Jihar Enugu a ranar 13/05/2021 da misalin karfe 2, suna zargin cewa an samu tashin gobara a Ofishin Obollo-Afor na Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), a Udenu LGA na jihar, Jami’an da ke aiki da sashin sun yi tsere zuwa wurin nan take, yayin da suka tuntubi Ofishin hukumar kashe gobara a yankin don hanzarta kashe wutar.”

A cewarsa, “binciken farko ya nuna cewa gobarar, wacce daga karshe aka kashe ta kafin ta iya yaduwa zuwa wasu ofisoshin da ke kusa da ginin, ta hanyar hada karfi da karfe da hukumar kashe gobara ta jihar, ‘yan sanda da masu bin doka da oda, mai yiwuwa ne ya haifar ta hanyar karuwa saboda ba da wutar lantarki ba zato ba tsammani.”

“A halin yanzu, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mohammed Ndatsu Aliyu, ya fara bincike sosai don kara gano hakikanin abin da ya haifar da gobarar da kuma asarar da aka tafka,” in ji shi.

Exit mobile version