Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta ce ta ceto rayuka da dukiyoyi 1,035 da kudinsu ya kai Naira miliyan 905 daga gobara 867 da aka samu a jihar daga watan Janairu zuwa Disamba, 2022.
Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano.
- Arsenal Ta Tsawaita Kwantiragin Saliba Da Saka Har Zuwa 2024
- Kasar Sin Ta Daidaita Manufarta Ta Kandagarkin Yaduwar Cutar COVID-19 Bisa La’akari Da Yanayin Da Kasar Ke Ciki
Abdullahi, ya ce mutane 166 ne suka rasa rayukansu, yayin da gobarar da ta kai Naira miliyan 358 ta salwanta a tsawon lokacin shekarar.
“Mun amsa kiran ceto 736 da kiran karya guda 208 daga mazauna jihar,” in ji shi.
Ya kuma ce hukumar ta samu haduran mota 575, yayin da kuma ta ceto dabbobi shida da suka makale.
Kakakin ya danganta faruwar gobarar da rashin kula da tukunyar iskar gas din girki da kuma amfani da na’urorin lantarki marasa inganci.
Ya shawarci jama’a da su guji ajiye man fetur a gida ko duk wani wuri da ba shi da tsaro.
“Wadanda suke dumama kansu a kasuwa ko kan titi a lokacin sanyi, su kashe wutar da isasshen ruwa don guje wa yanayin da ba a zata ba.
“Ya kamata iyaye su kasance masu lura da yaransu, musamman masu zuwa wanka tafki da kuma wasa a wurare masu hadari,” in ji shi.
Abdullahi ya kuma shawarci mazauna jihar da su ke kiran hukumar kashe gobarar da zarar wani abu na neman dauki ya taso.