Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,
A bisa ga konewar Babbar Kasuwar Sakkwato, Gwamnatin Jihar Ribas ta yi alkawalin bayar da tallafin tsabar kudi naira miliyan 500 domin sake gyara kasuwar wadda wuta ta yi wa mummunar illa a jiya Talata.
Gwamna Ezenwo Nyesom Wike a ziyarar jajantawa da ya kaiwa Tambuwal a yau ya bayyana cewar za a yi amfani da wani bangare na kudin domin tallafawa ‘yan kasuwar da gobarar ta shafa. “Gobarar ta girgiza ni matuka ainun domin duk abin da ya shafi Sakkwato ya shafi Ribas, don haka za mu yi kokari domin ganin an sake gina kasuwar.” In ji Wike.
Tun farko a yayin da ya zagaya da Gwamna Wike a sassan kasuwar da ta kone, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyyana cewar kasuwar da ta kone ta na da shaguna 16, 000 kuma kashi 60% sun kone bakidaya.