Wasu mutanen kauye sun tabbatar da konewar wasu mutum biyar, sakamakon kama wutar da wata tankar daukar iskar gas ta yi, wadanda suka yi kokarin kubuta, amma hakan ta gagara.
Tankar ta kama da wuta ne a garin Ifiekporo da ke karamar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta.
Wadannan mutane sun yi konewar da ba za iya gane su ba, an dai yi wannan hatsarin ne a kusa da gabar kogin Warri.
Majiyar ta ci gana da shaida mana cewa, wadanda suka konen sun yi kokarin ganin su kubutar amma dai hakan bai yiwu ba.
Majiyar ta kara da cewa, wadanda suka konen suna kusa da inda tankin iskar gas din ya kama da wuta, bayan kama wutar, sai aka ji wata fashe wa, wanda a lokacin ne wutar ta yi rimi, ta rufe wadannan mutane kuma ta kone su.
Tuni dai aka dauki gawar mutanen zuwa Warri.
Jami’an gwamnatin jihar Delta da suka halarci wajen da wannan abu ya faru, sun bayar da rahoton cewa, sun tabbatar da cewa, ba samu wanda ya mutu ba a wannan gobara, saidai yanzu haka mutum goma sha biyu na kwance a asibitin Ogiame Ikenwoli,Ubeji.
Da aka tuntubi shugaban kamfanin gidajen main a ‘Matrid Group’ Mista Fred Olomuro, ya tabbatar da faruwar wannan lamari da kuma muutuwar mutum biyar wadanda wannan wuta ta rutsa da su.