Wata tanka ɗauke da fetur (PMS) ta kife a ranar Lahadi a jihar Legas inda nan take ta kama da wuta. Gobarar ta bazu cikin sauri, ta laƙume aƙalla manyan motoci guda huɗu da aka ajiye a wajen Iyana-Isolo zuwa Oshodi.
Daraktan sashin hulɗa da Jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA), Taofiq Adebayo, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna gudun wuce gona da iri ne ya sa direban ya rasa iko da motar, abin da ya haifar da mummunar haɗarin.
- A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho
- Legas Ta Laƙume Aikin Naira Tiriliyan 3.9 Cikin Shekaru Biyun Tinubu
Cikin gaggawa jami’an LASTMA, tare da haɗin gwiwar ma’aikatan kashe gobara da jam’ian ƴansanda daga Aswani, da Ilasa da Mushin, da ma jami’an tsaro na unguwanni ne suka yi aiki tukuru wajen shawo kan gobarar kafin ta girmama.
Babban Daraktan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya tabbatar da cewa babu asarar rai, yana mai jaddada cewa hakan ya faru ne saboda saurin rufe hanyar da kuma dakatar da motoci daga Ilasa zuwa Oshodi. Ya gargadi direbobin manyan motoci da tankoki su kiyaye gudun wuce sa’a domin kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma buƙaci jama’a da su rika amfani da layin waya kyauta na LASTMA wajen sanar da kowanne irin hatsari ko matsalar hanya, domin hukumar ta ci gaba da kare lafiyar al’umma da kuma tabbatar da tsari a hanyoyin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp