Jama’a barkanmu da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa.
A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar Juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka:
Sako daga Aisha Ahmad
Assalamu alaikum!
Ina mika godiyata ga ma’aikatan gidan wannan jarida mai albarka tare da sakon gaisuwata da suka bani dama da na mika sakon gaisuwata na gode. Ina mika sakon gaisuwata ga Iyayena da yayyena da kannena ‘yan uwana mata da maza wadanda muka yi makaranta tare da su, al’ummar Musulmi baki daya, duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Juma’a lafiya. Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina tare da yi masa fatan alkhairi da fatan an yi Sallah Juma’a lafiya.
Sako daga Idris Muhammad
Assalaikum alaikum!
Al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na ina musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayye na da kanne na da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannensu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Bilkisu Musa
Assalamu alaikum! Ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na nesa ‘yan uguwarmu da wadanda muka yi makaranta tun daga kan firamare, Sakandire, Jami’a duk ina yi muku fatan alkhair da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Hassana Abba
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi, ina fatan Allah ya jikan mahaifiyata ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana amin ya Allah.
Sako daga Abubukar Haruna Ahmad
Ina mika sakon goron Juma’a ga al’ummar Musulmi gaba ki daya, da jamia’an tsaro dake kasar nan baki daya. Ina mika gaisuwata ga mahaifiyata Hajiya Lamee Musa, da mahaifina Alhaji Aliyu Isah. Ina mika sakon gaisuwa ga yayata Ummi, da kanwata Aisha, da yayana Faisal, da kanina Abdulrahman, da yaya na sadik. Da fatan sako na ya iso ku cikin koshin Lafiya.
Sako daga Zulaihat Musa
Assalamu alaikum!
Ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida dana waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana smin ya Allah.
Sako daga Aunty Mama
Assalamu alaikum! Â Ina mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan wannan gidan jarida na LEADERSHIP Hausa tare da mika godiya ta da suka bani dama da na mika sakon gasuwata na gode.
Ina mika sakon gaisuwata ga mijina da iyayena, ina fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga ‘yan ‘uwana yayyena da kannena da fatan suna cikin koshin lafiya sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Sadiya Sani
Assalamu alaikum! Ina mika sako gaisuwa ta ga mutanan gidan wannan jarida mai albarka tare da mika godiya ta da suka bani dama da na mika sakon gaisuwata na gide. Ina gaida iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki, abokan karatu da abokan aiki na da al’ummar Musulmi baki daya tare da barka da Juma’a da fatan an yi Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Ahmad Isa
Al’ummar Musulmi ina yi muku Sallama irin ta addinin Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi Ta’alah Wabarakatuhu! Ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na ina musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannansu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Abba Husain
Assalamu alaikum warahmatullah!
Ina mika sakon gaisuwa ga iyaye, ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kun yi Sallar Juma’a lafiya Tare da kai ziyara Allah ya sa haka amin, ina gaida kowa da kowa.