ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ku Kula Da Kyawawan Ɗabi’u, Su Ne Waɗanda Annabi SAW Ya Kira Duk Halitta A Kansu

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 months ago

Alhamdulillahi… kamar yadda duk musulmai suka yi imani cewa, littafin Alƙur’ani mai girma, wanda ubangiji tabaraka wata’ala ya saukarwa masoyinsa, kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW, ya zama gagara-badau, don haka, ya gagari duk masana, ta yadda suka gaza kai karshen ilimin da ke tattare acikinsa.

Duk nisan zamani da sauyinsa, za ka ga Alƙur’ani ya tattaro ilimin wannan zamanin. Don haka, ubangiji ke horo da cewa, “a zurfafa bincike acikinsa”, a wani wuri kuma cewa, “ka ce, ya ubangiji ƙara min ilimi”.

  • Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo
  • Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
  • Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus
  • ’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP
  • An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

A wannan makon, shafin namu mai albarka, tsakuro mana wani abu ya yi na ilimi wanda kyawawan ɗabi’u ke jagorantarsu, wanda ya yi daidai da fahimtar wannan karni mai cike da kimiyya da fasaha.

ADVERTISEMENT

Mu Kula Da Kyawawan Dabi’u, Su Ne Waɗanda Annabi SAW Ya Kira Duk Halitta a kansu.

Kyawawan ɗabi’u, sune waɗanda ke haɗa duk halitta, sune doka da za su zaunar da kowa lafiya, saboda sune hankali. In ɗan Adam ya yi kure a kan su, sai ka ji ana cewa, “wane ba shi da hankali”.

LABARAI MASU NASABA

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Don haka, shi addini ba shi da kayan dole, ba shi da bulala ko takobin dole, ƴanci kawai yake so, saboda abu ne na zuciya, “la ikraha fiddin – ba dole a cikin addini”, in baka bai wa zuciya dama ta karɓi abu da kanta ba, to ka ƙera wa kanka “munafuki”, da zarar ya samu dama, zai gudu, amma in aka bata dama, ta karɓi addini da kanta, to babu fargabar wata rana za ta gudu.

Musulunci ya fara samun ƙalubale ne a Fathu Makkata, yayin da Kuraishawa suka karɓi addinin ba cikin son ransu ba. An ga haka, a yayin yakin Hunaini wanda Annabi SAW ya tafi jim kaɗan bayan Fathu Makkata, bayan ya samu labari cewa, kusan soja dubu talatin (30,000) sun taru a Hunain suna shirin kawo masa hari.

Ruwaya ta zo da cewa, Annabi SAW ya zo Fathu Makkata da soja dubu 8 ko dubu 10, sannan ya ƙara da soja dubu 2 daga Makkah inda jimillar adadin sojan ya kama dubu 10 ko dubu 12, ana fara gwabza yaƙi, wannan mutanen na Makkah suka gudu, wanda hakan ya yi sanadin tarwatsewar sauran tawagar rundunar Annabi SAW, har sai da matayen mutanen Madina suka taso suka tarbi mazajensu da cewa, yaushe kuka fara guduwa ku bar Annabi SAW a filin yaƙi shi kaɗai? Ta kaka za ku biyewa waɗanda suka shiga addini ba da zuciya ɗaya ba!

A nan take, aka fahimci cewa, mutanen Makkah, ba da zuciya suka shiga addini ba, da jiki suka shiga.

Kar Kayi Magana A Kan Abin da Baka Da Ilimi A Kansa

Mai Diwani ya lissafo kyawawan ɗabi’u 10 wanda duk addinatai kusan suna kansu, sannan ya karo da wasu uku da suke gargaɗi.

Haram-haram guda 10 akan Muminai mabiya Annabi SAW, wadanda sun yi daidai a littafin Annabi Musa (AS), sun yi daidai da hikima ta Annabi Isah (AS), kuma sune hikima ta Lukmanal hakim:

Kar mu tara Allah da wani, kar mu kashe ƴaƴanmu don tsoron talauci, kar mu kusanci alfasha daga abin da ya bayyana da wanda ya buya, kar mu kashe rai wacce Allah ya hana, kar mu kusanci dukiyar maraya sai da abin da ya fi kyau, mu cika ma’auni, mu yi adalci a wurin magana, mu faɗi gaskiya ko da a kan abokanmu ne, mu cika wa Allah alkawari, sannan mu bi hanyar Ubangiji.

Wannan abubuwan da muka lissafo guda 10, kusan duk addinatai akansu suke babu saɓani, sai dai suratul Isra’i ta ƙara wasu guda Uku:

– Ciyarwa: ya dace mai hali ya taimaki abokin shi mabukaci, da naƙasasshe da ƴan gudun hijira.

– Kar ka yi magana a kan abin da baka da ilimi a kansa. Ba ka da ilimi akan siyasa, ka yi shiru, ba kada ilimi a kan kasuwanci, to shiru ya fi amfani.

– Kar ka yi girman kai.

Waɗannan abubuwan da aka lissafo, suna daga cikin hikima ta ubangiji da ya yi wahayi a gareka ya Rasulallahi.

Mumini Dole Ya Bi Direban Da Ya San Hanya Kuma Ya San Dokokin Tafiya (Shehi Masani)

Mai Diwani, ya ci gaba da karatu game da yadda Suratul Furƙan, ta lissafo kyawawan dabi’u, duk da cewa na kowa ne amma sun fi ƙarfi a kan Muminai ba gama garin Musulmai ba.

Ya dace ga Mumini ya yi tafiya sannu-sannu, ya bi dokokin hanya kamar yadda ake alamtawa a kan manyan hanyoyi domin kiyaye haɗɗura. Kamar yadda hakan yake a tafiyar zahiri, kuma haka yake a tafiyar ruhi. Mumini, dole ya bi direban da ya san hanya kuma wanda ya san dokokin tafiya (Shehi masani), wanda zai nuna masa yadda ake tafiya kan lamarin ubangiji, tun daga:

– Attakwa ta Islam: Attaubatu, Al’istiƙamatu, da Attakwa.

– Attakwa ta Imani: Assidku, Al’iklas, da Addumaninatu.

– Attakwa ta Ihsani: Almurakaba, Almushahada, da Alma’arifa.

Daga nan, ya cigaba da tafiya har ila masha Allah.

Don haka, sufanci fanni ne da yake a tsare, duk wanda ya ara ya yafa, sai kaga cakudi a lamarin shi. Sabida komai a rubuce yake kamar yadda aka rubuta duk alamomin hanya, misalin in kana tafiya zuwa wani gari, za ka riƙa ganin dokokin hanya a rubuce a bakin hanya, kamar tsarin yadda ake son direba ya yi gudu ko ya rage gudu, hanya samɓal ce ko akwai kwana, an kusa zuwa cikin gari ko an fita daga gari, wurin tsallakwar mutane ne nan ko dabbobi, da sauransu dai. Kamar yadda aka gindaya wannan sharuɗan a tafiyar zahiri, haka yake a tafiyar ruhi, da faɗin ubangiji, “wa ibadurRahmanillazina yamshuna alal ardi haunan…”

Har ila yau, Suratu Furkan ta yi kira ga Malamai su iya zama da wadanda ba su da ilimi, don su (malaman) zauna lafiya.

Sannan ta jaddada muhimmancin zaman lafiya, da kokari ga yin addu’a.

Kada Ka Wulaƙanta Kowa, Kuma Kada Ka Yarda Da Wulaƙanci

Mutunta kai, ko daraja kai, yana da matuƙar muhimmanci ga Mumini, ya dace daraja kansa tare da mutunta kansa. “Kada ka wulakanta kowa kuma kada ka yarda da wulaƙanci”, ba hakan yana nuna kaje ka yi faɗa ba ne, a’a, yana nufin ka ja da baya daga alaƙa da wulaƙantattu. Har a wurin mutanen kirki ma, kada ka yarda da wulaƙanci.

Har ila yau, suratul Furƙan ta nuna cewa, in an gayyace ka wurin shirme ko wuri mara mutunci, kada ka halarta, da faɗin ubangiji, “wa iza marru billagwi, marru kirama”.

Shehu Ismaila Umar Almadda (Mai Diwani), ya jaddada muhimmancin mutunta kai ne a yayin da yake cigaba da karatun Tafsirin Alƙur’ani mai girma acikin Suratu Namli, wanda yake gudanarwa a Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group, Kaduna.

Game da batun hikima ko zurfafawa a tunani, ko kai matuƙa a sani, duk inda aka ambaci hikima, sai kaga ƙanƙan da kai, da mutuntawa, kuma ta duk ƴanAdam ce, ba tare da la’akari da banbancin addini ko aƙida ba.

Don haka, waɗannan mutane masu hikima, akan ƙwaƙwalwa da tunani suke kullum, ya dace musulmai mu hankalta, mu koma baya don sanin tarihi. Da yawa wasu abubuwa da aka kafa cewa, sune Sunnah ba haka suke ba, tsabar rashin tunani ne wasu suka ƙirƙiro, da nufin rusa ƙwaƙwalwa da tunanin musulmai.

Ana cewa, “Wayewa, itace kasan abin da kake da shi da abin da waninka yake da shi, don kasan me zaka ƙara ko kuma alhamdulillahi, kai za ka ƙara masa”.

Abin mamaki, littafinmu (Alƙur’ani) shi ne ƙololuwar ilmi, kamata ya yi a ce, duk wannan ilimin na zamani daga wurin musulmai ya ke amma mune ƙarshe a wauta da koma-baya.

Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Komawa Ga Allah Ta Hanyar Yawaita Istigfari
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Kula Da Tarihi A Musulunci
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da ‘Ya’yansu Alkur’ani (2)

MASU ALAKA

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
Labarai

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro
Manyan Labarai

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya
Manyan Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

June 3, 2026
Next Post
Ta Hanyar Kyautata Fasahar Makamashi Kasar Sin Na Samar Da Damar Raya Kasa Ga Sauran Kasashe

Ta Hanyar Kyautata Fasahar Makamashi Kasar Sin Na Samar Da Damar Raya Kasa Ga Sauran Kasashe

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.