Jama,a barkammu da juma,a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma,a. Shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa. A you ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan anyi sallar juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar juma’a tare da kaiziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka:
Sako daga Habiba Tijjani:
Assalaikum alaikum!
Al’umar musulmi baki daya, ina yiwa kowa fatan alkhairi tare da fatan anyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na mamana da babana ina musu fatan alkhairi da fatan sunyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana kannena da fatan sunyi sallar juma’a lafiya. Ina gaida kannan mamana da kannan babana tare da yi musu fatan anyi sallar juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da juma’a.
Sako daga Zahara Murtala.
Assalamualaikum, ina yi wa kowa da kowa fatan alhairi a wannan rana ta Juma’a. Ina son amfani da wannan daman wajen mika gaisuwa da fatan alhairi ga iyayena Malam Murtala Umar da Malam Taibatu Bello. Ina kuma gaishe da kannai na Akeela Murtala da Khadija Murtala. Ina kuma gaishe da kannen mahaifiyata, RAMATU, Khadija, Amina, Bakir, Sani, Ahmad da kuma Adam. Ina gaishe da dukkan Al’umma musulmin Duniya. Allah ya zaunar da kasar mu lafiya. Amin
Sako daga Maryam Umar (Ummy).
Assalamu alaikum, al’umar musulmi baki daya ina muku sallama irin ta addinin musulunci. Ina yiwa kowa fatan alkhairi tare da farin jikin zagayowar wannan rana mai albarka ranar juma’a , da fatan anyi sallar juma’a Lafiya. Ina gaida mijina tare da fatan anyi sallar juma’a Lafiya, ina gaida iyayena tare da yimusu barka da juma’a ina gaida yayuna da kanne na da ‘ya’yana da fatan sunyi sallar juma’a Lafiya sai kawaye na tare da fatan sunyi sallar juma’a Lafiya.