Jama’a barka da juma’a da fatan kowa zai yi juma’a lafiya, kamar kowanne mako kafin naje ga bude sakonnin masu karatu sai na fara mika tawa gaisuwar, zuwa ga dukkanin al’ummar musulmi baki daya, ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki na gida dana waje, ina gaida abokan aiki da dukkanin jama’ar da ke gaida ni, sai gaisuwa ga sauran ma’aikata baki daya na wannan Jaridar ta Leadership musamman Edita na Abdulrazak Yahuza Jere.
Bari kuma naje ga sakonnin masu karatu:
Sako daga Ummulkhursum Nasir Jihar Kano:
Ina gaida Mamana da Babana, sannan ina gaida Halima Sale, Zakiyya Abdulsalam, khadija Lamin, Adele Mike, Mahdiyya Haruna, Fatan sun yi Juma’a Lafiya.
Sako daga Nabila Dikko:
SaÆ™on goron jumma’a na yau kai tsaye zuwa ga manyan mata ‘yan kasuwa, maganin kananun mata wanda suka yi fice gurin sayar da zafafan kaya, masu inganci wato ‘ARGUNGU ENTERPRENUERS’ ina muku fatan alheri, gaisuwar ban girma ga ‘yan uwana, masoyana da abokan arziki da fatan kun yi juma’a lafiya.
Sako daga Zahra’u Abubakar (Dr.Zahra) Jihar Kano:
Assalamu alaikum ina yiwa daukacin ma’aikatan Jaridar Leadership fatan alkairi sannan ina mika sakon gaisuwata zuwa ga kakata Ramatu ( Yaya) da ke karamar hukumar Isa a Jihar Sokoto, sannan ina mika sakon gaisuwata ga Ibrahim, baban Rumasa’u da Aisha, sannan ina mika sakon gaisuwata zuwa ga Mustafa Abban Sadik da kuma Mujittaba Abban Malam da kuma Auwal (A.A.Umar) baban Amir da Ameera, sannan ina mika sakon gaisuwata zuwa ga metron Habiba da Metron Asiya Nuhu Banmali Hospital alkairin Allah ya kai musu a duk inda suke, a karshe ina gaida Abdullahi Adamu Gwani Baban Amarya.
Sako daga Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor):
Ina miko sakon gaisuwata zuwa ga ‘yan ‘group’ din Taskira karrakataf dinsu, musamman ma Aunty Rabi’a da Nana Aisha maradi. Ina gaida yarana,
Fatima, khadija Abdulmumin da kuma Almustapha, sai ‘ya ta Habiba Abdulhadi (Iman),
Da fatan an yi juma’a lafiya.
Sako daga Maryam Ibrahim ‘Yar mutan Sakoto:
Da farko ina mika sakon barka da juma’a zuwa ga ayarin iyalan gidan Marigayi Alh Alu Achida da fatan dukkaninsu za su yi Juma’a lafiya, kana daga bisani ina mika sakon barka da juma’a dina zuwa ga ayarin Iyalan gidan Malam Shehu Usman Bubare da fatan suma za su yi sallar juma’a lafiya, daga bisani ina yiwa kafatanin ilahirin marubuta barka da juma’a, kama daga kanana har manya suma da fatan za su yi sallar juma’a lafiya, ina mika sakon barka da juma’a dina zuwa ga ‘Ya’yana abin alfaharina wato Aminu Dankaduna Amanawa da fatan shi ma zai yi juma’a lafiya, daga karshe ina yiwa kawayena fatan alkhairi da fatan za su yi sallar juma’a lafiya wato, Oummeenmust da Eshart kana da Shehyn Ta’o ban manta da Fatin Jamilu ba kana da Zubaidar Rabi’u daga karshe ina yiwa Uwanin Bukkoki fatan ta yi sallar juma’a lafiya.
Sako daga Yahaya Maikaza Kajiji 08080323435:
Salama’alaikum Editan jaridarmu mai albarka wato Leadership Ayau, ina son a bani dama in mika gaisuwar goron juma’a zuwa ga Kabiru Muhammad Sha’aibu gatan masu sauraron Bond FM da Honorable Altine Shehu kajiji da alhj. jinjiri mil12 da alhj. Ibrahim tsohon Ciyaman na kasuwar Alabo da Yakubu Waliyyi da Fatima Bintu dake sango da fatan sun yi juma’a lafiya, Madallah da ranar malaman makaranta ta duniya da majalisar dinkin duniya ta ware, hakan zai sa malamai su kara kaimi wajan fitar da duniya daga jahilci. Agefe daya kuma ina kira ga gwannatin kasarmu Najeriya da ta kara kaimi wajan ganin ta inganta rayuwar malaman makarantun kasarmu ta fuskar wadatasu da kayan aiki da albashi mai tsoka.
Sako daga Maryam Murtala Jihar Kano:
Ina gaida Mamana da Babana sannan ina gaida Mahadiya Haruna, ina gaida Zainab Aminu, Hafsat Abdulmudalib, Bilkisu Musa, Aisha Kabir Sheshe, Maryam Nafi’u, Munifa Abbas, Safiyya Salisu Tahir, Ina gaida Mamah, Rukayya Salis, Jamila Salisu, Anti Nana, Anti Fauziyya, da Ahmad, da afnan da Anti Rukayya, da Surayya. Da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Fatima Ali Musa Badawa Jihar Kano:
Ina gaida Mamana da Babana sannan ina gaida yayyena da kannena, ina gaida Rahma Sani Nuhu, ina gaida Fatima Ilyas Abubakar, Ina gaida Rabi’atu Abdul’aziz, ina gaida Rahma Muktar, ina gaida Amina Abdulkadir Isah, ina gaida Aisha Abdullahi Muhammad, ina gaida Maryam Haruna Salis, ina gaida Fatima Abdulkadir Ishak, ina gaida Zainab Labaran, ina gaida Khadija Bello Umar, sannan ina gaida Malamaina Maza da mata fatan sun yi juma’a lafiya.