Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

An Goyi Bayan Gwamnatin Tarayya Kan Yaki Da Rashawa

by Tayo Adelaja
September 16, 2017
in LABARAI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Kwamishiniyar Shari’ ta Jihar Kebbi, Hajiya Rakiya Haruna Ayuba, ta yabawa Gwamnatin Tarayya kan yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan, a cewarsa babu wata gwamnati da za ta samu zaman lafiyar gudanar da aiki matukar akwai bara gurbi a cikinta..

Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne a Birnin-kebbi, a lokacin da take gabatar da jawabin ga manema labarai na irin nasarorin da ma’aikatar da tke jagoranta ta samu, wanda kungiyar ‘ya jarida ta jihar kebbi, watau (NUJ) take shirya ga ma’aikatun gwamnatin Jihar Kebbi a kowane wata domin yada manufufin gwamnatin zuwa ga al’umma.

Hajiya Rakiya ta ce, “yakin da cin hanci da rashawa da Gwamnatin tarayya ke yi ya rage almundahana a ofisoshin gwamnati tun daga matakin kananan hukumomi har zuwa jiha, kuma ya taimaka wajen kawo zaman lafiya ga bangaren ilimi na kasar nan, haka zalika ya samar da daidaito a tsakanin al’umma.”

Har ila yau, ta bayyana cewa game da masu laifi dake jiran hukunci su 237 da ke tsare a gidajen yarin Jihar Kebbi daga shekara ta 2015 zuwa 2017, an magance wannan matsalar, musamman don ganin an rage cinkoson mutane a gidajen yarin.

“Gwamnatin da ta shude ta bari gidajen yarin sun cika makil, mutane suna jiran hukunci ko ba a gabatar da su a gaban kotu ba, suna nan kawai ajiye. Wannan sam bai dace ba, yana cikin abubuwan da ofishina ya fara mayar da hankali a kai lokacin da na kama aiki.” In ji ta.

A karshe ta ce, “matsalar masu laifi da ke jiran Shari’a ajiye a gidajen suna da yawa a Nijeriya, wanda Kebbi na cikin wadanda haka ya shafa, amma duk da haka, mun yi iya kokarin mu na rage yawan adadin lamarin zuwa mataki kadan.”

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Aka Gudanar Da Bikin Dashen Shuka Itace A Jami’ar ABU Zariya

Next Post

Rikici Ya Barke Tsakanin Kansiloli Da Shugaban Karamar Hukumar Kontagora

RelatedPosts

Dabbobi

Zamanin Kiwon Dabbobi A Sake Ya Shude – ACF

by Muhammad
7 hours ago
0

Kungiyar Ta Goyi Bayan Matsayin Gwamnonin Arewa Daga Abubakar Abba,...

Garkuwa

Neja Ce Kan Gaba Wajen Fuskantar Matsalar Masu Garkuwa Da Jama’a- Gwamna Bello  

by Muhammad
7 hours ago
0

Daga Muhammad Awwal Umar, Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya...

Barista

Barista Ahmad Ghazali Ya Zama Abin Koyi -Mansur Dandago

by Muhammad
7 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Watan Azumi na cikin lokutan da...

Next Post

Rikici Ya Barke Tsakanin Kansiloli Da Shugaban Karamar Hukumar Kontagora

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version