Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce duk wani yunkuri na neman ‘yancin kan yankin Taiwan na nufin rarraba yankunan kasar Sin, kuma goyon bayan wannan aniya katsalandan ne a harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar Sin da dokokin kasa da kasa.
Wang Yi, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin a birnin Beijing, yayin zantawa da takwaransa na Jamus Johann Wadephul, ya yi karin haske kan gaskiyar abubuwan da suka wakana a tarihi, da tushen shari’a dangane da batun Taiwan. Ya ce matsayin Taiwan na yankin kasar Sin abu ne a fili, kuma al’amuran da suka gudana a tarihi, da dokoki na hakika sun tabbatar da hakan.
Ministan wajen Sin ya kara da cewa, a baya bayan nan jagorar Japan mai ci ta furta wasu kalamai na shaci-fadi kan yankin Taiwan, wanda hakan ya yi matukar keta hurumin ‘yancin mulkin kai da tsaron yankunan kasar Sin, ya kuma sabawa alkawuran da Japan din ta yiwa Sin. Kazalika, hakan ya kalubalanci sakamakon nasarar da aka cimma a karshen yakin duniya na biyu, da odar kasa da kasa bayan yakin, tare da barazana ga zaman lafiya a nahiyar Asiya da ma duniya baki daya.
Wang Yi ya ce Sinawa da sauran al’ummun duniya masu kaunar zaman lafiya, na da alhakin kare sharudda, da yarjejeniyar tsarin gudanar da MDD, kuma suna da nauyin dakatar da Japan daga komawa manufar amfani da karfin soji, da yunkurin cimma burikan fadada ayyukan soji. (Saminu Alhassan)














