Abba Ibrahim Wada" />

Griezman Ba Zai Koma Barcelona Ba

Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Enrikue Cerezo, ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Antonio Griezman bazai bar kungiyar ba a wannan kakar mai zuwa Barcelona sabanin irin rahotannin da ake yadawa cewa yana son komawa Barcelona.

Duk da cewa a kakar wasan data gabata ya sake sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Atletico Madrid, rahotanni a kwana kwanan nan sun tabbatar da cewa dan wasan baya jin dadin zamansa a kungiyar bayan da yayi wasanni bakwai bai zura kwallo a raga ba.

A kwanakin baya kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kusa siyan dan wasan sai dai daga baya dan wasan da kansa yace bashi da niyyar barin kungiyarsa kuma yana son cigaba da zama domin kafa tarihi.

Sai dai wasu rahotanni a kwanakin baya sun bayyana cewa dan wasan ya fara dana sanin rashin komawa Barcelona a shekarar data gabata kuma aka bayyana cewa yanzu yana shirin bawa Barcelona hakuri domin su koma su sake nemansa.

“Babu wani dalili da zaisa mu siyar da Griezman a wannan kakar saboda dan wasan mune kuma zai cigaba da zama damu amma kuma ‘yan wasan da zasu tafi zasu iya tafiya amma shi dai muna tare dashi nan da shekaru masu zuwa” in ji shugaban kungiyar.

Griezman dai a wannan kakar ya zura kwallaye 18 cikin wasanni 39 daya bugawa kungiyarsa ta Atletico Madrid kuma a shekarar data gabata ya taimakawa kasarsa ta Faransa ta lashe kofin duniyar da kasar Rasha ta karbi bakunci.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ma dai tana zawarcin dan wasan wanda tun lokacin tsohon kociyan kungiyar, Jose Mourinho ya nemi da kungiyar ta siyo dan wasan amma dan wasan yace bazai bar inda yake ba.

Exit mobile version