Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
Kananan Hukumomin Mulkin Gudu da Binji da ke a Jihar Sakkwato ba su taba samun Kwamishina ba a tsayin shekaru 18 da farar hula suka kwashe a saman turbar Mulkin Dimokuradiya.
Dukkanin Gwamnatocin da aka yi a Sakkwato sun kawar da kai wurin nadin kujerar mukamin Kwamishina a Kananan Hukumomin Gudu da Binji. Gwamnatin Attahiru Dalhatu Bafarawa 1999-2007 da Aliyu Wamakko 2007-2015 da kuma Aminu Waziri Tambuwal a 2015 zuwa yau ba su dauko ko dan siyasa daya suka ba shi mukamin Kwamishina ba daga yankunan biyu.
Hakan na nufin duk wainar da aka ci a ka toya, Kananan Hukumomin Gudu da Binji ba su da wakilci a majalisar koli ta zartaswar lamurran Gwamnatin Sakkwato wadda ta kumshi Kwamishinoni zalla a tsayin wadannan shekarun. Karara hakan na nufin babu wanda zai tsaya masu ko ya yi masu wata hobbasa ta musamman a yayin zaman Majalisar Zartaswar Jiha.
Jihar Sakkwato ta na da kananan hukumomi 23. Baya ga Kananan Hukumomin Gudu da Binji, su kansu kananan hukumomin Rabah (Mahaifar Sardaunan Sakkwato) Shagari, Illela, Isah da kuma Gwadabawa ba su da wakilci a majalisar zartaswar Gwamnatin jiha a zubin mulkin da ke gudana a yau.
A Gwamnatin Wamakko da ta gabata Karamar Hukumar Yabo kadai ta samu Kwamishinoni har guda hudu masu karfin iko da fada a ji haka kuma yau a Gwamnatin Tambuwal akwai Kwamishinoni guda shida bakidaya a Karamar Hukumar Sakkwato Ta Arewa wadanda ke da cikakken ikon sanyawa da fitarwa a yayin da Gudu da Tangaza ba su da kowa a Majalisar Zartaswar Gwamnati.
A Sakkwato ta Arewa kadai Gwamnatin Tambuwal ta nada Sa’idu Umar a matsayin Kwamishinan (Kudi) Muhammad Bello Abubakar (Filaye da Gidaje) Abdulkadir Jeli (Yada Labarai) Abdullahi Maigwandu (Ci-gaban Yankunan Karkara) Tukur Alkali (Lafiyar Dabbobi da Gandun Daji) da kuma marigayi Nasir Zarummai (Kimiya da Fasaha)
A bayyane yake cewar galibi Gwamnonin Jihohi a Nijeriya ba su cika duba cancanta wajen nada Kwamishinoni ba. A lokuta da dama wadanda Gwamnoni ke nadawa a matsayin Kwamishinoni ‘yan siyasa ne wadanda suka taka muhimmiyar rawa ga ci- gaba da bunkasar siyasar Gwamnan Jiha da ke jan zaren mulki da kuma wadanda iyayen gida suka bayar domin a nada kan mukamin; ire-iren wadannan iyayen gida inma su zama a fannin siyasa da kasuwanci ko kuma mulki da sarauta.
Ayar tambayar da masu fashin bakin al’amurran yau da kullum ke neman amsa a yau ita ce shin babu ‘yan siyasar da suka taka muhimmiyar rawa tun daga 1999 zuwa yau a Kananan Hukumomin Gudu da Binji? Ko kuwa Kananan Hukumomin biyu ba su da iyayen gidan da ke da kima da tasirin da za a ba su damar bada sunan Kwamishina daya zuwa biyu? Ko kuwa a’a bakidaya a Gudu da Binji babu wanda ya cancanta ya hau kujerar Kwamishina ko kuwa an ba su ne suka ce a’a a bari sun gode?
Domin amsa wannan tambayar LEADERSHIP A YAU ta tattauna da fitaccen jigon dan siyasar yankin, kazalika Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Gudu, Hon Bello Wakili Bachaka wanda bai yi kasa a guiwa ba wajen bayyana ra’ayinsa da cewar ko kadan ba rashin cancanta ne dalilin da yasa Karamar Hukumar Gudu ba ta samu Kwamishina a inda aka fito da inda ake ba.
“Tabbas a shekaru 18 na mulkin farar hula a Nijeriya ba mu taba yin Kwamishina a Gudu ba. Gwamnatocin da suka gabata duka ba su waiwaye mu a kujerar Kwamishina ba. Gwamnatin Attahiru Bafarawa da ta Sanata Aliyu Wamakko duka sun ba mu mukamin Mashawarci na Musamman ga Gwamna amma ba su ba mu Kwamishina ba.”
Hon Wakili Bachaka ya kuma bayyana cewar suna da fitaccin ‘yan siyasar da suka cancanta su zama ‘Yan Majalisar Zartaswar Gwamnatin Jiha. “Daga cikin al’ummar Gudu akwai wadanda sun karantar da wasu wadanda Kwamishinoni ne a yau. Haka ma a bangaren siyasa muna da gogaggin ‘yan siyasar da suka ji gishiri ta yadda gudunmuwar da al’ummar mu suka bayar a jiya kuma suke bayarwa a yau a bayyane take.” Inji Bachaka.
A yayin da yake bayyanawa LEADERSHIP A YAU ra’ayinsa, fitaccen matashin dan siyasar Gudu, Honarabul Abdullahi Ubandawaki Awulkiti ya bayyana cewar bai kamata a ce karamar hukumar su ba ta taba samun wakilci a Majalisar Zartaswar Gwamnatin Jiha ba.
Hon Ubandawaki wanda ya taba rike mukamin Kansila ya bayyana ra’ayinsa da cewar “Ra’ayina shine abin mamaki ne a ce akwai karamar hukumar da ba ta taba samun Kwamishina ba a wannan siyasar da ake a kai, amma sai ga shi a Gudu an bar mu baya duk kuwa da irin gagarumar gudummuwar da muke takawa a siyasance. Idan har za a baiwa wata karamar hukuma Kwamishina hudu ko biyar ita kadai to kai tsaye za mu ce ba a yi mana adalci ba. Don haka muna fatar a wannan karon za a yi mana adalci ta hanyar waiwayo mu.” Inji Honarabul.
A Karamar Hukumar Binji wadda ita kanta ba ta taba rike kujerar Kwamishina ba a tsayin shekaru 18 na mulkin Dimokuradiya, mabambantan al’ummar yankin sun koka kan yadda Gwamnatocin da suka gabata da ita kanta Gwamnatin da ke mulki a yau suka yi fatali da su a wannan muhimmiyar kujerar.
Abubakar Maikulki ya bayyana ra’ayinsa da cewar “Ba dole ba ne a kowane zubin siyasa sai kowace Karamar Hukuma ta samu Kwamishina ba, amma idan wata karamar hukuma na da biyar ko shida a lokaci daya, wata kuma ba ta da ko daya ka ga kenan babu adalci.”
Ya kara da cewar “Akalla ya kamata idan wata Gwamnati ta shude, Idan wata ta zo sai ta gyara kuskuren siyasar da aka yi domin a samu maslaha da daidaito.” A cewar sa.
Shi kuwa Muhammad Sani Gawazzai cewa ya yi “Matsalar rashin Kwamishina ta dade tana ci mana tuwo a kwarya a Binji bisa ga yadda aka mayar da mu saniyar ware. Domin muna taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar kowace Gwamnatin siyasa a wannan jihar amma har yau ba a taba ba mu Kwamishina ba. Muna kira ga Gwamna Aminu Tambuwal da ya duba wannan matsalar ya yi gyaran da ya dace a lokaci mafi dacewa.” Ya bayyana.
Ya zuwa yanzu dai akwai kujerar Kwamishinoni biyu da ke jiran nada wadanda za su dare saman kujerun wato Kwamishinonin ma’aikatar Kimiya da Fasaha wadda Kwamishinanta Hon. Nasiru Zarummai ya karbi kiran mahallacinsa watanni 18 da suka gabata a ranar 5 ga Maris 2016 da kuma ta ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Kwamishinanta Sahabi Isa Gada a matsayin sabon Jakadan Nijeriya a kasar Tanzaniya.