Hausawa su kan ce, ”Guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni.” Tunani na dogaro da kai da karfin zuci da wannan magana ta nuna, ba zai taba zama na tsohon yayi ba.
A jihar Enugu ta kasar Najeriya, akwai wani nau’in abinci na gargajiya da ake kira Okpa, wanda ake yinsa da garin gujiya. A baya a kan kalli abincin a matsayin na matalauta, ganin yadda ake samunsa cikin sauki. Idan wani ya sha shayi da Okpa, maimakon abincin Turawa irinsu Biscuit da burodi, to, za a yi masa dariya. Sai dai daga bisani wani sarki mai suna Christian Onoh, ya daidaita yanayin da Okpa din ke ciki, inda ya gayyaci manyan mutane don su sha shayi da cin Okpa tare, har ma ya mai da Okpa a matsayin kyak din da ake ci yayin bikin ranar haihuwarsa.
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars N2m, Ta Dakatar Da Ɗan Wasanta
- Naim Qassem Ya Zama Sabon Shugaban Hezbollah
Bisa kokarinsa na yayata wannan abinci, sannu a hankali ya zama nau’in abinci mai farin jini a jihar Enugu da Najeriya baki daya. Sa’an nan binciken da masu nazarin kimiyya da fasaha suka yi, shi ma ya nuna cewa, Okpa din wani nau’in abinci ne mai gina jiki sosai.
Wannan labari da aka bayyana shi cikin wata makalar da aka wallafa kan shafin yanar gizo na jaridar Punch ta kasar Najeriya ya nuna mana cewa, ya kamata a nuna karin imani, yayin da ake kula da wasu abubuwan gargajiya.
Hakika ci gaban zaman al’umma ya kan sa a kara darajantar abubuwa na gargajiya. A wannan fanni za mu iya duba misali na kasar Sin. A baya, lokacin da kasar ta zama karkashin hare-haren da wasu kasashe masu karfi suka kai mata, da fuskantar danniya a fannin tattalin arziki, da kutsa kai ta fuskar al’adu, Sinawa sun tantace al’adunta na gargajiya bisa kwatantawa da na kasashen yamma cikin zurfi, har ma sun yi la’akari da maye gurbin bakaken Sinanci da haruffan Turanci, don tabbatar da saukin rubutawa a lokacin. Sai dai a kasar Sin ta wannan zamani, mutanen kasar na kokarin kare wurare masu tarihi, da nazari a kansu, da gadon fasahohin al’adu. Yayin da matasa ke kallon tufafi, da kide-kide, da sauran alamu masu salon gargajiya a matsayin abubuwa masu farin jini. Kana duk wani birnin kasar na kokarin raya gidajen ajiyar kayayyakin tarihi, da tsoffin tituna da ungwanni, don nuna tarihi da al’adu na musamman da yake da su.
To amma ko mene ne ya sa ake darajantar al’adun gargajiya? Saboda asalin tunanin wata kasa yana cikin al’adunta na gargajiya. Dole ne a yi nazari kan al’adu da tunani na gargajiya, domin ta haka ne za a iya samun wata turbar raya kasa mai dacewa. Misali, manufar zamanantarwa ta kasar Sin ta kunshi bangaren samun jituwa tsakanin dan Adam da muhallin halittu, sai dai asalin bangaren shi ne tunanin Taoism na kasar, na ”duk wani abu da ni a hade suke.” Ban da haka, yadda tunanin zamanantarwa na kasar Sin ke dora muhimmanci kan tabbatar da wadatar daukacin al’umma, shi ma ya samu asalinsa ne daga tunanin gargajiyar kasar Sin na tabbatar da daidaituwa tsakanin al’umma.
Ban da haka, yadda ake kokarin kare al’adun gargajiya da raya shi, yana da amfani na musamman ga yunkurin warware matsalolin da duniyarmu ke fuskantar. Tun fil azal, Sinawa sun jaddada muhimmancin tsarin kasancewar duniya karkashin mallakar daukacin kasashe da al’ummun duniya. Saboda haka a ganin kasar, kamata ya yi, a samu daidaito da zumunta tsakanin mabambantan al’ummu. Wannan ra’ayi ya zama daya da tunanin Ubuntu dake yaduwa a nahiyar Afirka, wanda ya jaddada bukatar samun kauna, da huldar cude-ni-in-cude-ka tsakanin mutane.
A wannan zamanin da muke ciki, wadannan tunanin gargajiya na Sin da Afirka sun zama matsaya daya ta raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya, wanda ya tabbatar da yiwuwar kawo karshen rikici da nuna bambanci, da kare zaman lafiya da yanayin ci gaba a duniya.
A zahiri, ta hanyar dogaro da kai, da kokarin kare al’adun gargajiya, da cudanya tsakanin mabambantan al’adu, za a samar wa duniya da daukacin dan Adam karin abubuwa masu yakini, da tabbatar da makomarsu mai haske. (Bello Wang)